Shugaba Donald Trump ya sanar da janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria.
Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙarin haske kan wannan matsaya a birnin Riyadh na Saudiyya inda yake ziyarar aiki.
Trump ya ce zai bai wa Syria damar tsayawa da ƙafafunta, bayan buƙatar gaggawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman ya miƙa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ya soma yada zango a Saudiyya a rangadin kwanaki huɗu da yake yi a ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Trump ya ɗauki matakin da ya ba wa kowa mamaki na janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria, a jajibirin ganawarsa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar Ahmad al-Sharaa a Saudiyya.
Dama dai al-Sharaa, da ya hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, yana ɗaukar matakin diflomasiyya a ƙasashen Larabawa da na Turai don daina mayar da ƙasarsa saniyar ware.
Takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba a lokacin da Assad ke kan karagar mulki, ya yanke ƙasar Syria daga tsarin hada-hadar kuɗi na duniya tare da daƙile zuba jari da cinikayyar ƙasashen waje, lamarin da ya kawo cikas ga yunƙurin sake gina ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Amurka ta ƙulla yarjejeniyar biliyoyin daloli da Saudiyya
A ɗaya hannun, Trump da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman sun rattaba hannu kan abin da aka bayyana a matsayin “yarjejeniyar hulɗar tattalin arziki”, ba tare da yin cikakken bayani kan yawan kuɗin da ta ƙunsa ba.
Sai dai, jami’an ƙasashen biyu sun bayyana cewar takardar fahimtar junar ta shafi fannonin tsaro, makamashi, da ma’adanai da horon ’yan sanda.
Bayanai na cewa Trump ya ƙulla yarjejeniyar kasuwanci ta biliyoyin dala da Saudiyyan, bayan ziyarar mai cike da tarihi da ya kai ƙasar a wannan Talatar.
Cikin yarjejeniyoyin da ƙasashen biyu suka ƙulla akwai ta dala biliyan 142, don cinikayyar makamai, abin da ke zama wani ɓangare na dala biliyan 600 na hannun jari da Saudiyya ta zuba a Amurka.
Baya ga wannan kuma, yarjejeniyar ta ƙunshi ta samar da Iskar gas da sauran makamashi na dala biliyan 14 da miliyan 200 sai jirgin sama ƙirar Boeing 737-8 kan dala biliyan 4 da miliyan 800.
Kazalika shugabannin biyu sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi sama da 10, da suka haɗar da musayar bayanai tsakanin jami’an tsaro, fannin shari’a da kuma musayar al’adu.
Haka kuma shugabannin biyu yayin tattaunawa tsakaninsu, sun faɗaɗa batu kan makamin nukiliyar Iran da kuma yaƙin da ke faruwa a tsakanin Isra’ila da Hamas.
Da yake bayani, shugaba Trump, ya ce ya amince cewa akwai kyakyawar alaƙa tsakanin Saudiyya da Amurka, kuma kasashen biyu suna kaunar juna, don haka akwai buƙatar su haɗa hannu don haɓɓaka tattalin arzikin juna.