✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta matsa wa ƙasashe da ke fuskantar haraji su amince da Starlink

Amurka ta matsa wa wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su  amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a…

Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su  amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu.

Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump.

Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton sakonnin waya na Ma’aikatar Harkokin Waje.

Sakonnin sun nuna yadda ofishin Jakadancin Amurka da ma’aikatar suka matsa wa ƙasashe don su kawar da duk wata cikas ga kamfanonin tauraron dan Adam, yana mai ambaton kamfanin Starlink da sunanta, kamar yadda jaridar Post ta ruwaito.

Takardun ba su nuna cewa gwamnatin Trump ta buƙaci a ba da fifiko ga Starlink a musayar rage haraji ba, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Amma sun nuna cewa Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio, ya umurci jami’ai da su matsa ƙaimi don samun amincewar ka’idoji ga kamfanin tauraron dan Adam na Starlink, mallakar Elon Musk.