Shugaban Amurka, Donald Trump ya isa ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda tuni ya sauka a Riyadh a jirgin Air Force One.
Shugaban na Amurka ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri.
Trump zai gana ne da Mohammed bin Salman a filin jirgin sama na Sarki Khalid da ke Riyadh a kusa da hotunan wasu daga ckin mambobin iyalan sarauta na Saudiyya
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ma zai kasance a cikin taron.
Bayan Saudiyya, Trump dai na shirin kai ziyara ƙasashen Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa daga ranar Talata zuwa Alhamis na wannan makon.
Shugaban Amurkan na wannan ziyara ta kwanaki huɗu a ƙasashen Gabas ta Tsakiya domin yauƙaƙa dangantaka da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikin makamai na biliyoyi har ma da tattaunawa kan batun yakin Gaza da shirin nukiliyar Iran.
Mista Trump na tare da attajirin Amurka kuma shugaban kamfanin ƙera motocin Tesla, Elon Musk da kuma wasu manyan muƙarraban gwamnati.
Wannan ce ziyararsa ta biyu tun bayan hawa kan karagar mulkin Amurka baya ga halartar jana’izar tsohon shugaban Darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis a birnin Rome na ƙasar Italiya.