✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri ne

Tuni dai ’yan sanda suka tsare mahaifin domin yi masa tambayoyi yayin da bincike ke ci gaba kan wannan lamari mai ban tausayi.

Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne.

Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti,  Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti.

Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa.

Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura da motsi a wata bishiya da ke kusa da shi, sai ya harba bindiga yana zaton biri ne. Bayan ya yi harbin sai ya gano cewa ya harbi dansa da ke kan bishiyar har lahira.

Tuni dai ’yan sanda suka tsare mahaifin domin yi masa tambayoyi yayin da bincike ke ci gaba kan wannan lamari mai ban tausayi.