Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan.
Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ambaliyar da ta faru a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, sakamakon ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya da ya yi sanadin rasa rayuka, bacewar mutane, da lalacewar gidaje, gonaki, da kayan more rayuwa.
Ya yaba da agajin gaggawa daga Gwamnatin Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da kuma kokarin hukumomin agaji wajen aikin ceto da tallafa wa wadanda abin ya shafa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi kira da a hada kai don kawo ɗauki cikin gaggawa da kuma samar da mafita mai ɗorewa, yana mai cewa: “Wannan bala’i ya nuna bukatar daukar matakan da za su hana sake afkuwar irin wannan annoba.”
- Layya da hukunce-hukuncenta a Musulunci
- Gwamnatin Tinubu na amfani da talauci a matsayin makami — Atiku
Ya kuma tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa wajen tallafa wa waɗanda abin ya shafa tare da fatan a samu zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.