Wata tsohuwa mai suna Misis Bui Thi Loi ‘yar kasar Vietnam mai shekara 75 ta yi ikirarin cewa, ba ta ci wani abinci mai nauyi ba a cikin shekaru 50, a maimakon haka tana rayuwa ne kawai da ruwa da abubuwan sha kamar lemon kwalba da sauran abin sha.
Bui Thi Loi, ‘yar garin Loc Ninh commune ce a lardin Kuang Binh a kasar Bietnam, tana da kyan siffa sosai a shekarunta, wanda abincinta ya zama abin mamaki.
- Kurakuran da ake yi a kwalliya cikin rashin sani
- Mataimakin fasto ya kashe shi a saman mimbarin coci
Tsohuwar ta dage cewa tana rayuwa a kan ruwa da abubuwan sha na tsawon rabin karni kuma ba ta taba sha’awar abinci mai nauyi ba.
Lamarin dai ya fara ne a 1963, lokacin da wata walkiya ta gifta mata a lokacin da ita da wasu mata ke hawa wani dutse domin jinyar sojojin da suka jikkata a lokacin yaki.
Karar sautin tsawar ta yi sanadin sumewarta, duk da ta tsira, amma ba ta taba komawa yadda take a baya ba.
Kwanaki bayan haka ba ta ci komai ba, bayan ta dawo hayyacinta, sai kawayenta suka fara ba ta ruwa.
Bayan ‘yan shekaru da faruwar walkiyar, Misis Bui Thi Loi ta ci gaba da cin abinci da canza salon ci, musamman kayan marmari, saboda danginta da abokanta sun damu kansu, amma ba ta taba jin bukatar irin wannan abinci ba.
A cikin 1970, ta nisanci abinci mai nauyi sosai, ta dogara kawai ga ruwa da abubuwan sha a matsayin abinci.
Firinjinta ya cika da kwalaben ruwa da abubuwan sha kamar lemukan kwalba.
Matar mai shekara 75 ta yi ikirarin cewa, kamshin abinci kadai ya isa ya tashi hankalinta, kuma duk da cewa takan yi wa ‘ya’yanta girki, amma a zahiri ba ta taba cin girkinta ba daga wancan lokacin.
Yanzu ‘ya’yanta sun girma sun koma waje da cin abinci, dakin girkinta yana yin kura.
Wani abin sha’awa shi ne, saboda yanayin abincin da take ci, ba za ta iya shayar da ‘ya’yanta nono ba, sai dai ta nemi nonon wasu.
Duk wani likita zai gaya muku cewa, rukunin abinci yana da mahimmanci ga rayuwa mai kyau, amma Bui Thi Loi abincinta da ya zama ruwa da abubuwan sha ya isa ya kiyaye lafiyarta da samun kuzari.
A cewar likitoci daga Tsangayar Abinci mai Gina Jiki a Asibitin Abota na Vietnam Cuba a Dong Hoi, abubuwan sha masu ruwa-ruwa masu sukari suna taimakawa wajen samun kuzarin jiki da sauri a lokutan bukatar hakan da kuma tallafa wa aikin tsarin narkewar abinci a jiki.
Duk da haka, sun jaddada cewa, abin sha na iya zama hadari ga lafiyar dan Adam kuma yana iya haifar da matsaloli kamar kiba, ciwon sukari, hawan jini da cututtukan zuciya.
Al’amarin Misis Bui Thi Loi ya shahara a Bietnam, kasar da irin wannan abu ba bakon ba ne.
Alal misali, a farkon wannan shekarar, an taba samun wani rahoto game da Thai Ngoc, wani manomi mai shekara 80 wanda ya yi ikirarin cewa, bai yi barci ba a cikin shekaru 60.
Duk da haka, a cikin duka biyun, har yanzu ba a tabbatar da ikirarin ta hanyar kimiyya ba.