✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurakuran da ake yi a kwalliya cikin rashin sani

Idan ba a gyara kwalliya ba, sai a ga fuskar mutum tana kama da ta dodo.

Akwai kurakurai da dama wadda mata suke yi wajen yin kwalliya ba tare da sanin hakan kuskure ba ne.

Ya kamata a kiyaye idan an zo shafa kayan kwalliya a fuska, musamman wajen sanya gazal da hodar fandesho da janbaki da sauran kayan kwalliya wadanda ba su dace da kalar fatar mutum ba.

A yau na lissafo irin kurakuren da mata ke yi wajen kwalliya. Idan ba a gyara ba, sai a ga fuskar mutum tana kama da ta dodo.

• Shafa hodar fandesho da bai dace da fatar mace ba: Sau da yawa sai a ga mace ta yi kwalliya da hodar fandesho da bai dace da launin fatarta ba.

Ya kamata a sami launin fandesho da ya dace da launin fatar mace kafin a yi amfani da shi.

• Shafa kayan kwalliya a fuska mai gautsi: Idan aka shafa kayan kwalliya a fuska ba tare da shafawa fuskar mai kadan ba, lallai kwalliyar ba za ta yi kyau ba.

Man jiki ko na fuska na gyara fata saboda haka, ya kamata ana shafa man fuska kafin shafa hoda.

• Idan kina da labba manya bai kamata ki cika labbanki da kazal ba. Domin yin hakan na kara fitar da girman labbanki.

Amma idan ke mai kananan labba ce za ki iya bin labbanki da gazal din baki (lip liner).

• Amfanin Gazal a gira: Idan ke mai cikakkiyar gira ce , bai kamata ki dada wata gazal a kan girarki ba.

Sai dai idan ke ba mai cikakkiyar gira ba ce, za ki iya cika girarki da gazal wanda kalarta ta yi daidai da gashin girarki.

• Idan za a shafa hodar ‘blush’ a tabbata cewa ana da farar fata domin wannan hodar tafi dacewa da mai farar fata ce.

• A tabbatar da cewa an ja gira daidai a kowane ido domin ba a son wata girar ta yi sama dayar kuma ta yi kasa. Yin hakan na bata kwalliyar mace sosai.