✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan kwalliya 6 da fata ke bukata

Yawan shafa irin wadannan mai na haifar da kuraje

Mun iske kanmu da nau’o’in man shafawa da mata da dama ba su san da me ake hada su ba. Su dai daga ganin ya yi kyau sai a ce zai yi wa fata kyau.

Yawan shafa irin wadannan mai na haifar da kuraje wadanda ba su barin fuska. Kuma ko da sun bar fuska sai a ga tabon na nan ba ya bata.

Don haka a yau na kawo muku abubuwan kwalliya shida wadanda ko a gida za a iya hada su don samun fata mai laushi kuma mara kuraje.

  • Man zaitun: Yana dauke da sinadaran rage maiko a fuska. Don haka yana da kyau idan za a sake yin kwalliya a samu auduga a tsoma a man zaitun a rika goge fuskar da ita kafin a sake yin watakwalliyar. Yin haka na hana fesowar kuraje a fuska.
  • Kwakwa: Sai a ga mace fara kyakkyawa, amma da za a taba hannunta sai a ji kamar tana faskare ko surfe tsabagen tauri. Idan ana da irin wannan matsalar, sai a samu kwakwa a kankare bayanta sannan a markada da ruwa kadan a tace a sa a firiji. Idan ta yi sanyi sosai sai a rika shafawa a tafin hannu tana sa fatar hannu laushi.
  • Zuma da sukari: Idan mutum na fama da fata mai yawan saba musamman fatar fuska, sai a hada zuma da sukari a wuri guda, sai a shafa a fuska na tsawon minti 30 kafin a murza a fuska. Yin hakan na cire fatar da ta mace a fuska don ba sabuwar fata waje. Idan an gama sai a wanke da ruwan dumi. Abubuwan kwalliya shida da fata ke bukata
  • Kindirmo: Yana sa fatar fuska laushi da sulbi. A samu kindirmo a shafa a fuska na tsawon minti 30 a kullum kafin a kwanta barci. Yin haka na kashe kowace irin kwayar cutar da take fesowa a fuska ko a fata.
  • Kwai: A samu ruwan kwai a cire kwaiduwar a rika bugawa har sai ya yi kumfa. A shafa a gashin kai na tsawon awa daya ko rabin awa sannan a wanke da man wanke gashi. Yin haka na cire daudar da ke cikin gashi da kuma hana gashi karyewa.
  • Fiya: Shi ma yana gyara gashi sosai. A kwaba shi ya yi laushi sannan a shafa a fatar kai don hana fesowar amosanin ka. A bari a fatar kai na tsawon minti 30 kafin a wanke da ruwan dumi.