✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa

Ba a fayyace yadda ainihin awakin suka hau saman tsaunin Santa Barbara tun a farko ba.

Masana kimiyya suna ƙoƙarin fahimtar yadda garken awaki ke rayuwa a wani tsibiri da ke Arewa maso gabashin Brazil fiye da ƙarni biyu (shekara 200) ba tare da samun tsaftaccen ruwan sha ba.

Ba a fayyace yadda ainihin awakin suka hau saman tsaunin Santa Barbara tun a farko ba, wanda ɗaya ne daga cikin tsibirai biyar masu aman wuta da suka haɗa da tsibiran Abrolhos, kimanin kilomita 70 daga gaɓar tekun Bahia, amma masana kimiyya sun yi imanin cewa, ’yan mulkin mallaka ne suka kawo su, suka bar su a wurin.

Dabbobi kamar irin su awaki da alade da kaji ana kiwon su ne don samun ingantaccen abinci, amma galibi ana barin su a baya lokacin da mulkin mallaka ya gaza.

An dai adana rubutun kasancewarsu a tsibirin Santa Bárbara fiye da shekaru 250, bisa ga bayanan tarihi, wanda ke da ban mamaki, idan muka yi la’akari da cewa, karamin tsibirin ba shi da sanannun hanyar samun ruwa.

Duk da wannan “rashin samun ruwa,” awakin sun yi ta kara yawa da bunkasa a busasshen tsibiri mai iska.

A watan da ya gabata, Cibiyar Kula da Kare Halittu ta Chico Mendes (ICMBio), wacce ke kula da gandun dajin ruwa na Abrolhos, ta ɗauke awaki 27 na ƙarshe a Santa Barbara.

Hakan na zuwa ne bayan da aka tabbatar da cewa, kasancewarsu zai yi illa ga ma’aunin muhallin tsibirin, musamman ma ya shafi nau’in halittun tsuntsayen teku guda bakwai da ke haihuwa a yankin.

Duk da haka, ba a ɗauke dabbobin ba saboda masana kimiyya suna son yin nazarin su, musamman yadda suke iya rayuwa ba tare da ruwa ko kadan ba.

“Mun yi imanin cewa, suna da wata baiwa ta rayuwa ta musamman don tsira a wurin, inda shugaban gandun dajin ruwa na Abrolhos, Erismar Rocha ya ce, “idan da ba a kula da yawan dabbobin ba, da sun mamaye tsibirin duka.”

Abin sha’awa shi ne, a cikin dukan shekarun da masana kimiyya suka yi nazarin awakin na Santa Barbara, ba su taba ganin su suna shan ruwa ba, wanda ya haifar da tambayar, “Ta yaya suke rayuwa a wurin sama da karni biyu?”

A wannan lokacin, masana za su iya yin hasashe ne kawai.

Wasu sun yi imanin cewa, wataƙila awakin sun yi ta shan ruwan teku ne kuma a wannan yanayin suke rayuwarsu zuwa tsawon wannan shekarun, yayin da wasu ke ganin suna cin tsirrai da furannin bedroega, waɗanda shukoki ne masu yawan ruwa da ake samu a Santa Bárbara, don rayuwar dabbobi.

Amma awakin Santa Barbara ba kawai suna rayuwa a can ba ne, suna jin dadin rayuwa a yankin.

Masu bincike sun ba da rahoton cewa, yawancin dabbobin da ake haifa a tsibirin tagwaye ne, wanda ke nuna cewa, awakin suna rayuwa cikin koshin lafiya.”

Ta hanyar nazarin awakin tsibirin Santa Bárbara, masana kimiyya na Brazil suna fatan gano sirrin matsananciyar juriyarsu, wadda za ta iya taimakawa wajen samar da sababbin nau’o’in da suka fi dacewa don tsira daga ƙalubalen sauyin yanayi da kuma daidaituwa a yankuna masu bushewa, kamar Arewa maso Gabashin Brazil.