Ana tuhumar wata ma’aikaciyar kamfanin masaka a Jihar Goias ta ƙasar Brazil da laifin saka wa abokan aikinta guba bayan ta yi jayayya da su a kan abin da matar ta kira da rashin adalci wajen ƙarin matsayi da kamfanin ya yi.
Lamarin ya faru ne a wata masana’anta da ke Abadia de Goias, wani gari a yankin Goiânia Metropolitan.
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal
- Iran ta mayar wa Amurka martani kan barazanar kai mata hari
’Yan sanda sun yi iƙirarin cewa, kyamarar daukar hoto cikin sirri (CCTV) ta kama wadda ake zargin mai shekara 38 tana buɗe wasu gorunan abin sha, wanda daga bisani wata ma’aikaciya ta sha, inda ta ji wani zafi a makogwaronta.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, an sami wani nau’in ɗanɗano mai ƙarfi a cikin ruwan, wanda ke nuna cewa, wacce ake zargi da laifin tana son zuba wa abokan aikinta guba.
Shaidu sun bayyana cewa, matan biyu abokan juna ne, amma dangantakarsu ta yi tsami bayan ɗaya daga ciki ta samu ƙarin girma, wanda bai yi wa wadda ake zargi da laifin daɗi ba.
Sun yi ta jayayya, wanda ake zargin lamarin ya kai ga matakin zuba gubar.
’Yan sandan yankin sun shaida wa manema labarai cewa, wanda ake zargin mai shekara 38, ta kuma shiga ɓangaren da ake ajiye sinadarai na kamfanin, ba tare da izini ba.
An yi imanin cewa, ta haka ne aka gano ta yi amfanin da sinadaran a matsayin guba.
Bayan ɗaya daga cikin ma’aikatan ta sha, ta gano cewa akwai matsala, inda ta kira motar ɗaukar marasa lafiya, aka garzaya da ita asibiti domin duba ta, amma ta warke sarai, sai dai likitoci sun ce, an yi yunƙurin kashe ta.
‘Yan sanda sun kama wadda ake zargin a ranar 27 ga Fabrairu, bayan sun duba kyamarori na CCTV don gano abin da ake zargin ta, kuma ta amince da gurbata abin shan ga abokan aikinta bayan sun yi wata jayayya.
Mai yiwuwa za a tuhume ta da laifin yunƙurin kisan kai, wanda ke da hukuncin ɗaurin shekar 6 zuwa 20 a gidan yari.
