✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu

Rahotanni sun bayyana cewar sojoji sun shawo kan lamarin bayan shafe tsawon lokaci.

Wasu direbobin manyan motoci sun rufe hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta da ke Jihar Kogi domin nuna fushinsu bayan jami’an tsaro sun harbi ɗaya daga cikinsu da kuma mataimakinsa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’an tsaro suka harbi mutanen biyu saboda sun ƙi tsayawa a wajen binciken da aka tsayar da su.

Sai dai, babu wanda ya mutu sakamakon harbin.

An garzaya da su asibiti domin ba su kulawar gaggawa.

Hakan ne, ya sa sauran direbobin suka fusata, suka toshe bakin gadar Ganaja da ke babbar hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta.

Sun ƙi ɗauke motocinsu har sai da sojoji suka iso wajen domin kwantar da tarzomar.

Rufe hanyar ta haddasa cunkoso mai yawa, inda matafiya da ma’aikata suka kasa zuwa wuraren aikinsu.

Wasu ma’aikata sun yi tafiya mai nisa a ƙafa, yayin da wasu suka koma gida suka haƙura da zuwa wajen ayyukansu.

Aliyu Dansabe, wani ma’aikaci, ya ce: “Na yi tafiya mai nisa daga rukunin gidaje na Governor Idris Wada har zuwa ofishina, kimanin kilomita bakwai.

“Lamarin ya gajiyar da ni sosai kuma ya tayar min da hankali. Muna godiya da zuwan sojoji da suka shawo kan lamarin.”

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da cewa an shawo kan lamarin.