✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi

An ba da rahoton cewa ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan kwanan ɗalibai da ke cikin harabar kwalejin  guguwar ruwan saman ta haddasa mummunar…

An samu rahoton cewa guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic), Idah a Jihar Kogi, inda ta ɓarnata  kadarori da gine-gine da dama.

Rahoton na cewa, wata mummunar guguwar ruwan sama da ta biyo bayan ruwan sama da aka kwashe tsawon sa’o’i ana yi a ranar Laraba ce ta haddasa barnar, inda ta lalata rufin gine-gine da tagar gine-gine da dama a makarantar.

Ana cikin haka, an ba da rahoton cewa ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan kwanan ɗalibai da ke cikin harabar kwalejin  guguwar ruwan saman ta haddasa mummunar ɓarna.

Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya Idah, Dokta Yakubu Usman, ya ce, “Wannan abu ne mai ban tsoro ga Kwalejin a irin wannan lokaci, muna baƙin ciki da irin ɓarnar da guguwar ta yi.

“Har yanzu muna kan tantance irin ɓarnar da guguwar ta yi domin sanin asarar kuɗi wajen gyarawa da kuma dawo da wuraren da suka lalace yadda suke.

“Ya zuwa yanzu matakin ɓarnar ya kai ga Gwamnatin Tarayya ce kawai za ta iya shiga tsakani a iya fitar da cibiyar daga wannan yanayin cikin sauri”.

Dakta Usman ya ƙara da cewa, cibiyar za ta yi duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafin da ya dace ga wuraren da abin ya shafa domin ɗalibai su ci gaba da harkokin karatu ba tare da ɓata lokaci ba