Wani mutum mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan da samu labarin cewa matarsa ta haifi jarirai ’yan uku a asibitin koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lokoja babban birnin Jihar Kogi ranar Juma’a.
Shaidu sun ce, mutumin da ya ji cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya mata uku, sai ya faɗi ya suma a harabar asibitin nan take.
- Zazzaɓin Lassa da sanƙarau ya kashe mutum 366 a jihohi 24 – NCDC
- Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni
Jami’an asibitin da masu jajantawa sun yi wa mutumin agaji inda cikin gaggawa aka samu ya farfaɗo.
Jim kaɗan da farfaɗowarsa, Muhammed, wanda aka ce ya kasance mai neman aikin yi na tsawon shekaru, ya ce labarin ya haɗa da farin ciki da baƙin ciki a gare shi.
Ya ce, “tunanin samun damar biyan kuɗin asibiti da kuma ɗawainiyar kuɗi na jariran da aka haifa uku ne ya dame ni. da jin labarin haihuwarsu nan take, lamarin ya sa na faɗi ƙasa na suma.”
“Na gode wa Allah da wannan abin al’ajabi, amma ina cikin ruɗani da baƙin ciki, ba mu sa ran haihuwar ’yan uku ba, a halin yanzu ba mu da kuɗi da ƙarfin biyan kuɗin asibiti, balle mu kula da jarirai uku a lokaci ɗaya.
“Wannan albarkar haihuwar tana da girma, amma hakan nauyi ne. Ba ni da ko da kuɗin sayan abincin jarirai. Ban san ta inda zan fara ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, suna faman gudanar yadda za su rayu; kuma an shirya haihuwar jariri guda ɗaya ne, don haka muka gaza biyan kuɗin yin hoton cikin don sanin ‘jarirai nawa ne saboda ƙarancin kuɗi.