Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan.
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki.
- Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete
- Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin.
Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar musu da tashin hankali.
“Mun kaɗu ƙwarai da yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a Nijeriya, da kuma rashin tabbas da ke biyo bayan kashe-kashen.
“Lokacin yin Allah-wadai ya wuce, yanzu matakin gaggawa ya dace gwamnatocin dukkanin matakai su ɗauka domin kawo karshen masifar nan.
“Mun san cewa tsaron kasa na hannun gwamnatin Tarayya ne, amma mu sani gwamnatin kowanne mataki na da alhakin tsaro da walwalar jama’arta, musamman gwamnonin jihohi.
“Bai dace aikinku ya tsaya a yin tituna da tarukan bukukuwa ba. Gwamnatin gaskiya ita ce wacce ta kafu akan kare rayukan al’umma, tabbatar da doka da oda, da kuma raba su da wahala.” In ji shi.
Daga nan ya yi kira ga gwamnatocin jihohin da su taimaka wa yunƙurin gwamnatin tarayya a ɓangaren tsaro ta hanyar samarwa da tilasta bin dokoki da sauran tsare-tsare a matakin unguwanni.