Tsohon Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Access Holdings, Herbert Wigwe ya rasu a haɗarin jirgin sama a Amurka.
Bayanai sun ce attajirin yana cikin wani jirgi mai saukar ungulu ne tare da matarsa, dansa da wasu fasinjoji uku lokacin da tsautsayin ya faru a yankin California.
- Jihar Zamfara na fuskantar ibtila’in cutar gubar dalma
- Maniyyatan bana su cika kudin kujerarsu kafin ranar Litinin — Hukumar Alhazai
Jaridar New York Times ta tabbatar da faruwar lamarin ba tare da fitar da sunayen fasinjojin da ke cikin jirgin ba.
Wata majiya mai tushe daga bangaren bankin a Najeriya ta bayyana cewa Herbert Wigwe, babban jami’in gudanarwa na kungiyar Access Holdings Plc, ya yi hatsarin jirgin saman mai saukar ungulu a Amurka, ranar Juma’a, da wasu mutane biyar a California.
Jirgin ya faɗo kusa da wani gari mai iyaka tsakanin Nevada da California a daren Juma’a.
An kuma ruwaito cewa Herbert Wigwe na kan hanyar zuwa Las Vegas don kallon Super Bowl, wasan zakarun lig na shekara-shekara na Hukumar Kwallon Kafa ta Ƙasa (NFL) ta Amurka.