Tsohuwar mai kula da dakin ajiyar kudi na bankin Guarantee Trust (GTB), Bolaji Agbede, ta zama shugabar rikon Rukuncin Bankin Access.
An nada Mis Bolaji Agbede ne bayan mutuwar tsohon shugaban kamfanin, Herbert Wigwe a hatsarin jirgin sama tare da matarsa da dansa da kuma tsohon shugaban hukumar canjin kudi ta Najeriya, Abimboloa Ogunbanjo, a kasar Amurka.
Sanarwar kamfanin nan ranar 12 ga watan Fabrairun 2024, ta ce “Hukumar Daraktocin Access Holdings Plc ya nada Ms Bolaji Agbede a matsayin mukaddashiyar babban jami’in gudanarwa, sakamakon rasuwar Herbert Wigwe, a ranar 9 ga Fabrairu, 2024.
“Nadin ya dogara da amincewar Babban Bankin Najeriya (CBN,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren Kamfanin, Sunday Ekwochi.
Wace ce Bolaji Agbede?
Kafin yanzu, Ms Agbede ita ce babbar Darakta ce mai mai kula da tallafa wa harkokin kasuwanci.
Mis Elegbe na da akalla shekaru talatin na ƙwarewa a harkar aikin banki da ba shawarwarin kasuwanci.
A shekarar 1992 tsohuwar dalibar ta Jami’ar Legas ta fara aiki a 1992 a bankin Guaranty Trust inda ta yi a bangarorin bankin kasuwanci da na gudanar da ayyuka, har ta kai matsayin manaja a 2001.
Ta kuma taba zama mai kula da dakin ajiyar kudi da kuma manajan hulda da jama’a a GTB.
Daga GTB ta koma kamfanin ba da shawara kan kasuwanci na JKG Limited, matsayin Babban Jami’iar Gudanarwa.
A shekarar 2003 ta koma bankin Access a matsayin mataimakin babban manaja kuma mai kula da huldar bankin na kamfanonin masu harkar sinadarai.
Ta zama shugabar kula da ma’aikata na rukunin bankin Access a shekarar 2010.
Awatan Yunin 2022 aka nada ta a matsayin babban darektan Access Holdings bayan bankin ya samu daukaka zuwa rukunin kamfani.