Jami’in kula da na’uar cirar kudi (ATM) na reshen Bankin Access ya shiga hannu kan sace kudade daga asusun musu ajiya a bankin a Jihar Katsina.
Asirin ma’aikacin da ke aiki a reshen bankin da ke yankin Daura ya tonu ne bayan sace Naira milyan 18 daga asusun masu ajiya.
Ana zargin jami’in, mai mukamin Mataimakin Mai Kula da ATM ne a bankin, ya sace kudaden ne ta hanyar hada baki da wani abokinsa wanda shi ma ma’aikacin bankin ne da ke garin Kafur, wanda shi kuma ya zambaci shugabansa har ya sace kudaden.
Asirin ya tonu ne bayan bincike a sashen, inda aka gano Naira miliyan 10 a asusunsa na bankuna daban-daban, da kuma tsabar kudi Naira dubu 366 a hannunsa.
- Gwamnatin Kano ta magantu kan yadda jami’an tsaro suka mamaye Fadar Sarki Sanusi II
- Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe
Kakakin ’yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da kama wadanda ake zargin.
Ya shaida wa manema labarai cewa da zarar sun kammala bincike za su iya keyar wadanda ake tuhumar zuwa kotu.