An tabbatar da rasuwar mutum huɗu, bankuna sun ƙone tare da wasu gine-gine bayan gobarar wata tankar mai a yankin Agbor da ke Ƙaramar Hukumar Ika ta Kudu da ke Jihar Delta.
A ranar Lahadi ne mummunan hatsarin ya auku a kan tsohuwar hanya Legas zuwa Asaba, inda motar man ta yi adungure a kusa da wani reshen bankin First Bank ta kama da wuta.
Mutane da dama sun jikkata baya ga asarar rayuka da maƙudan dukiyoyi a hatsarin. A cewar shaidu, hatsarin ya auku ne a yayin da direban motar yake ƙoƙarin juyawa a kusa da reshen bankin da ke Agbor.
Wani ganau ya ce bankuna biyu da wasu gine-gine sun kama da wuta baya ga mutanen da aka yi asarar.
Gwamnan Jihar Delta, Sherif Oborovwori, ya mika ta’aziyya game da lamarin, yana mai jinjina wa jami’an kiwon lafiya da masu lashe gobara da sauran masu aikin ceto bisa gudunmawa da suka bayar.