✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno

Gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, da kuma raba daruruwa da muhallin su.

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Lahadi, ta laƙume ƙauyukan Wanori, Sarari, da Nuguri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Aminiya ta rawaito cewa gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, da kuma raba daruruwa da muhallin su.

Lamarin dai ya tilasta mazauna ƙauyen Wanori yin ƙaura domin gujewa gobarar da ke ci gaba da yaɗuwa.

Ibtila’in da ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton ba a gano musabbbinsa, ya ƙara dagula wa al’ummar ƙauyen lissafi, kasancewar an samu makamancin hakan a baya, ga kuma ‘yan ta’addan Boko Haram da ke tilasta su yin gudun hijira.

Duk ƙoƙarin da manema labarai suka yi domin jin ta bakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Konduga, Honarabul Abba Ali Abbari, ya ci tura, sai dai wasu mazauna garin sun ce an gano gawarwakin maza biyu, wadanda aka binne tun a ranar Lahadi.