✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe

Sanatan ya ce tallafin wani ɓangare ne na rage wa waɗanda gobarar ta shafa raɗaɗi.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe.

Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari.

Sanata Lawan, ya jajanta wa mutanen da suka yi asarar dukiya sakamakon gobarar.

Ya ce haƙƙinsu ne su taimaka wa juna, kuma zai ci gaba da ƙoƙari don ganin cewa wadanda abin ya shafa sun samu tallafin da ya dace.

Ya bayyana cewa wannan tallafin zai ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na samar da agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa, tare da taimaka musu, su farfaɗo daga ɓarnar da gobarar ta yi musu.

A cewarsa, an ware Naira miliyan 12 da buhunan shinkafa 150 ga Ƙaramar Hukumar Machina, wanda za a raba a garuruwan Ngabarawa, Dole, Ghana, da Damai.

Ƙaramar Hukumar Nguru, za ta karɓi Naira miliyan biyar da buhunan shinkafa 50, wanda za a raba wa al’ummar Askema da Mirba.

Ƙaramar Hukumar Yusufari, za ta samu Naira miliyan 10 da buhunan shinkafa 100, wanda za a raba wa mutanen Tulo-Tulo da Isufuri.

Sanata Lawan, ya buƙaci gidauniyar SAIL Foundation, wacce ke kula da rabon tallafin, da ta tabbatar da gaskiya da adalci wajen raba wa waɗanda suka cancanta.

Ya kuma yi addu’a Allah Ya ba waɗanda abin ya shafa ikon jure wannan jarabta da sauƙi a gare su, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan.