✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kona motoci 10 a garejin Borno Express

Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motoci na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane…

Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce.

Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin.

Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a wannan lamarin, wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ya samu raunuka yayin da yake kokarin kashe gobarar.

Wani ganau ya ce, “Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas — inda wani kara mai ban tsoro ya sa ma’aikata da matafiya a yankin suka yi ta gujegujen domin tsira.”

Ya ƙara da cewa, “Hanzarin da hukumar kashe gobara ta yi ne ya hana lamarin ƙara ƙazancewa. Sun isa da sauri kuma sun yi nasarar shawo kan gobarar.”

Kwamishinan Sufuri da Makamashi na Jihar Borno, Aliyu Buba Bamanga, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru amma ya ƙi yin tsokaci.

Kwamishinan ya ce, “Muna jiran Mai Girma Gwamna Babagana Umara Zulum nan ba da jimawa ba. Ba zan so yin magana kafin wata sanarwa ta hukuma daga gare shi ba.”

Wani ma’aikacin garejin ya shaida wa wakilinmu cewa galibin motocin da abin ya shafa motocin bas ne masu ɗaukar mutane 18 da ake yi wa gyaran yau da kullum, da kuma wasu ƙalilan da ake yi musu manyan gyare-gyare.

“Mun auna arziki  da gobarar ba ta shafi wurin cajin motocin lantarki da ke kusa ba, da gobarar ta kai can, da munin lamarin ya ɓaci.”

Garejin gyaran motocin, wanda Kamfanin Sufuri na Borno Express ke gudanarwa, yana da alhakin kula da motocin zirga-zirgar jama’a na jihar.

Wannan lamarin ya faru ne kwana daya kacal bayan wata gobara ta cinye dubban gidaje a wasu yankuna huɗu a Alau, Jihar Borno, ind ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da lalata dukiya.