More Podcasts
Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato.
An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo.
Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu.
Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i?
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
- DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
Wannan na cikin batutuwan da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.
Domin sauke shirin, latsa nan