✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

A gefe guda kuma akwai ayar tambaya game da sharuɗan da asusun ke gindaya wa ƙasashen Afrika.

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), ya fitar da jerin ƙasashe 10 da suka fi kowa cin bashi a Nahiyar Afirka.

Wannan rahoton na IMF ya zuws ne a lokacin da ƙasashen Afirka ke fama da matsalolin bashin da suka karɓa domin magance matsalolin tattalin arziƙin da ya shafe su.

Abin mamaki, Najeriya ba ta cikin jerin ƙasashen 10 da suka fi cin bashi a Afirka, duk da yawan bashin da ta ke karɓa.

Ƙasashen da suka fi kowa cin bashi su kan yi amfani da bashin domin cike giɓin da ke cikin kasafin kuɗaɗensu.

Ko da yake IMF yana bayar da lamuni, tare da sanya sharuɗa masu tsauri ga ƙasashen da suke neman wannan taimako, wanda ya haɗa da janye tallafi, rage darajar kuɗi da sauransu.

  • Masar: Ƙasar ta karɓo bashin dala biliyan 9.45, yayin da take cikin matsalolin tattalin arziƙi.
  • Kenya: Ta karɓi bashin dala biliyan 3.02 domin bunƙasa tattalin arziƙinta da magance matsalolin cikin gida.
  • Angola: Ta karɓi dala biliyan 2.99, domin ƙayyade farashin mai da kuma inganta tattalin arziƙinta.
  • Ghana: Ta karɓi dala biliyan 2.25, saboda tana fama da matsalolin darajar kuɗi da kuma matsi na tattalin arziƙi.
  • Ivory Coast: Ta karɓi bashin dala biliyan 2.19 domin aiwatar da tsare-tsaren bunƙasa ƙasar.
  • Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo: Ta karɓi dala biliyan 1.6 domin magance matsalolin tattalin arziƙi.
  • Habasha: Ta karɓi dala biliyan 1.31 domin magance matsalolin tattalin arziƙin da ke addabarta.
  • Afirka ta Kudu: Ta karɓi dala biliyan 1.14 domin magance matsalolin tattalin arziƙi.
  • Kamaru: Ta karɓi dala biliyan 1.13.
  • Senegal: Ta karɓi dala biliyan 1.11 domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar.

Dogaro da kuɗaɗen IMF na ƙara bayyana matsalolin hada-hadar kasuwanci da kasashen Afirka ke fuskanta, inda suke ƙoƙarin warware matsalolin kasafin kuɗi da kuma cimma burin ci gaba mai ɗorewa.

Haka kuma, wannan yanayi yana nuna yadda ƙasashen Afirka suke cikin damuwa da kuma yadda suke dogaro da tallafin IMF don shawo kan matsalolinsu.

Duk da cewa IMF na taimaka wa ƙasashen, amma kuma yana janyo ayar tambaya game da yadda wasu sharuɗan tallafin ke shafar ‘yancin ƙasashen wajen aiwatar da tsare-tsarensu na bunƙasa tattalin arziƙi.