✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun mai damfarar masu cirar kudi a ATM ta cika

Wani matashi da ke yaudarar masu zuwa cire kudi a na'urar cirar kuxi ta banki (ATM) ya kwashe musu kudade ya shiga hannu a yankin…

Wani matashi da ke yaudarar masu zuwa cire kudi a na’urar cirar kuɗi ta banki (ATM) ya kwashe musu kuɗaɗe ya shiga hannu a yankin Daura da ke Jihar Katsina.

An gano cewa matashin yana kuma yaudarar mata da sunan zai kwana da su, inda yake sace katin ATM dinsu, ya kwashe kuɗin da ke bankinsu.

Matashin da dubun nasa ta cika yakan yaudari jama’a ne da sunan zai taimaka musu a bakin ATM, inda yake fakar idanunsu ya sauya musu katinsu da suka ba shi da wani da ke hannunsa.

Idan ya sa katin da ya canza musu, dasga baya sai ya ce musu katin ba zai cire kudi a lokacin ba, bayan sun tafi kuma sai ya sa ainihin katinsu ya kwashe musu kudin da ke bankinsu.

Asirin matashi mai shekaru 37 daga Jihar Sakkwato, ya tonu ne a yayin da wani dan sanda da ke aiki a wani banki da matashin ya yi ta kokarin danfarar wasu mutane.

Ganin take-takensa, sai dan sandan ya titsiye shi, har  a karshe dubunsa ta cika. Bayan an caje shi kuma aka samu katin ATM 14 da bayanan wasu daga cikin mutanen da ya kwashe wa kudi ta wannan hanyar.

Binta Yunusa na daga cikin mutanen da suka farkon matashin, ta ce,  inda ya kwashe mata kudi Naira 75,000, sai kuma wani mai suna Fatahu Makiyi da ya kwashe wa naira dubu 49.

An gano cewa matashin ya yaudari mutane da dama ta wannan hanya har na jimlar kudi Naira miliyan biyu da dubu dari 705 a lokutta dabam-daban.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa manema labarai faruwar hakan, inda ya ce da zarar sun kammala bincike za su iya keyar wadanda ake tuhumar zuwa kotu don fuskantar hukunci.