Hukumar Tattara Haraji ta jihar Gombe ta kulle bankin Access saboda taurin bashi biyan harajin da ya taru a kan su ya kai kimani Naira miliyan 118.
Da yake hira da manema labarai a harabar bankin jim kadan da kulle shi ranar Litinin, Shugaban hukumar, Abubakar Inuwa Tata, ya ce bankin ya ki biyan harajin da ke kansa ne tsakanin shekarar 2008 zuwa 2019.
- Kungiyar matan Kannywood za ta maka Sarkin Waka a kotu
- ’Yan sanda sun cafke Abba Kyari sa’o’i bayan NDLEA ta ba da shelarsa
Inuwa Tata, ya ce bisa umurnin doka sun tura wa bankin takardar sanarwa na tsawon kwana 30 kan su biya kudin, amma suka cewa komai har kwanakin suka wuce.
A maimakon haka a cewarsa, sai suka kai hukumar kara a kotu a ranar 20 ga watan Maris din 2021,inda kotun ta kori karar ta kuma umurce su da su biya hukumar kudin, wanda gaza biyan ya sa suka rufe shi.
Ya ce, “Kotu ta yanke hukunci ne a kan cewa banki ya biya harajin da ke kansa a ranar 10 ga watan Fabarairun 2022, kan cewa bankin ya biya mu ko mu kulle bankin.”
Shugaban hukumar ya kuma yi kira ga masu biyan haraji da kungiyoyi da su bi tsari da dokar da gwamnatin Jihar Gombe ta fitar na tsarin biyan haraji .
Ya kuma ce za su bude bankin da zarar ya biya bashin don ya ci gaba da gudanar da hada-hadar kasuwanci.
Wasu kwastomomi da muka zanta da su a harabar bankin sun nuna takaicinsu kan yadda bankin ya gaza biyan haraji, har ta kai an kore su a lokacin da suke neman biyan bukatarsu.
Sai dai yunkurin wakilinmu na jin tab akin bankin ya ci tura, inda suka ki cewa uffan a kan lamarin.