Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmawa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.
Sarki Sanusi ya yi jawabin ne a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’in bankin da aka gudanar a otel ɗin Eko da ke Jihar Legas.
- Mahara sun sace dalibai 100 da firinsifal a Kaduna
- Gwamnan Filato Ya Sa A kamo Wadanda Suka Kashe Makiyayi
Cikin hawaye da shassheka, Sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar Herbert Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.
Ya ce tsohon babban jami’in Bankin Access ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.
Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce a lokacin har jirgin sama Mista Herbert ya tanadar masa don ɗaukarsa daga Kano zuwa Legas.
“A lokacin da na samu matsala a Kano, wata shida kafin a sauke ni, na kira shi na faɗa masa halin da ake ciki, sannan na ce masa, ‘Herbert na san irin ƙoƙarin da kake yi wajen magance wannan matsala, amma na san sauke ni za a yi.
“Sai ya ce min ‘mai martaba’, kada ka damu. Duk abin da ya faru kar ka damu muna tare da kai.
“A ranar da na ji sanarwa a rediyo cewa an sauke ni, sai na kira shi na ce masa ina son zuwa Legas.
“An yi sanarwar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, zuwa tsakar rana Herbert ya tanadar min da jirgi a filin jirgin sama na Kano.
“Sai dai a lokacin an tsara cewa za a kaini zaman gudun hijira na shekaru masu yawa, daga nan sai na saka iyalina cikin jirgin tare da tura su Legas.
“Ban yi waya da shi ba, amma ya tarbe su tare da sauke su a otal, kafin daga baya ya sama musu muhalli, inda suka kwashe watanni suna zaune kafin na komo Legas don ci gaba da zama tare da iyalaina.”
Sarki Sanusi ya kuma ce ya yi tunanin zai riga Wigwe rasuwa, kuma a dalilin son ’ya’yansa su samu ilimi mai nagarta, ya damka wa Wigwe amana da wasiyyar kulawa da su bayan rayuwarsa.
“Na yi tunanin zan riga Mista Herbert rasuwa saboda haka kimanin shekaru biyu da suka gabata na sanya duk abin da na tara a cikin asusun ajiya saboda karatun ’ya’yana.
“Ina da burika masu yawa amma babban abin da na sa gaba a matsayina na uba shi ne tabbatar da cewa idan na rasu za su samu ingantaccen ilimi.
“Na ce wa Herbert kai ne za ka jibinci lamarin wannan asusun ajiyar da na buɗe saboda ilimin ’ya’yana domin na san cewa ko da na mutu ban bar kuɗi ba, za ka ilimantar da ’ya’yana,” a cewar Sarki Sanusi cikin hawaye.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 9 ga watan Fabarairun bana ne Herbert Wigwe ya rasu a wani haɗarin jirgin sama a Jihar California da ke Amurka.
Herbert Wigwe ya rasu tare da matarsa Doreen da ɗansa da Chizzy da Manajan Darakta na kasuwar hada-hadar hannayen-jari ta Nigerian Exchange Group Abimbola Ogunbanjo da kuma matuƙan jirgin biyu.
Ana iya tuna cewa, a watan Maris na 2020 ne Gwamnan Kano na wancan lokaci, Abdullahi Umar Ganduje, ya tube rawanin Sarki Muhammadu Sanusi II ya kuma nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.