Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta sayar da gidaje 753 da aka ƙwato daga tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Wannan sanarwar ta fito ne daga Ministan Gidaje, Ahmed Dangiwa, a ranar Talata yayin da yake karɓar takardun mallakar gidajen daga hannun Hukumar EFCC.
- Mun dakatar da sanya tallan magungunan gargajiya a fina-finai – Abba
- ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano
Gidajen suna cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ministan, ya gode wa EFCC saboda yadda ta ke aiki tuƙuru wajen yaƙar cin hanci da rashawa.
A cewar sanarwar da kakakin ma’aikatar, Salisu Haiba, ya fitar, an tabbatar cewa waɗannan kadarori na daga cikin dukiyoyin da aka ƙwato daga hannun masu almundahana da kuɗaɗen jama’a.
Idan ba a manta ba Emefiele na ci gaba da fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci da rashawa, tun bayan sauke shi daga shugabancin CBN.