✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Zamfara na fuskantar ibtila’in cutar gubar dalma

Binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa dimbin masu hakar zinare na ci gaba da aikace-aikacensu.

A sakamakon mataki na wucin-gadi da kungiyar nan mai ba da tallafin a fannin lafiya wato Médecins Sans Frontières a harshen Faransanci ta dauka na rage aikace-aikacenta da kuma kwashe wasu daga cikin ma’aikatanta daga kananan hukumomin Anka da Zurmi a Jihar Zamfara, al’ummomin kauyukan da ibtila’in gubar dalma da shafa a shekarun baya sun koka.

Kungiyar wadda a ke yi wa lakabi da Doctors Withour Borders a Turance ta rage aikace-aikacen ta tare da kwashe manyan ma’aikatanta musamman ’yan kasashen waje daga Karamar Hukumar Anka zuwa Karamar hukumar Talatar Mafara sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankin na Anka.

Haka zalika a watan Disamban bara, kungiyar ta rage yawan ma’aikatanta da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara sakamakon hareharen ’yan bindiga.

Duk cewa matakin rage aikace-aikacen da yawan ma’aikatan na wacin-gadi ne, al’umma mazauna garuruwan Bagega da Abare da Dareta da ’Yar Galma da Nasarawa da ke kananan hukumomin Bukkuyyum da Anka wadanda ibtila’in cutar gubar dalma ta shafa a shekarun baya na ci gaba da bayyana fargabarsu ta sake dawowar cutar.

Hakan ya sa al’ummomin suke kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su dauki matakai na gaggawa domin toseh duk wata kafa da ka iya haifar da dawowar cutar wadda mazauna yankin suka fuskanta a 2010.

Wani mazaunin yankin na Bagega, Malam Abubakar Isa ya bayyana cewa “A lokacin da aka yi cutar gubar dalma a shekarar 2010, mata da yawa sun rika haifar jarirai nakasassu da suka hada da makafi da shanyewar barin jiki da tamowa da matsalar kwakwalwa.

Haka kuma manya ma sun fuskanci matsalar ido da matsanancin zazzabi. Ya kara da cewa taimakon gaggawa da aka samu daga kungiyar Doctors Without borders tare da tallafin Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara ne ya kawo karshen wannan ibtila’in.

A nasa bangaren, Malam Muhmad Auwal ya tabbatar wa Aminiya cewa wasu daga cikin alamomin cutar gubar dalma sun fara bayyana a yankunan sakamakon ci gaba da hakar zinare da akeyi ba tare da daukar matakan kariya ba.

“A sakamakon haka wanna cutar ta gubar dalma ta fara dowowa musamman a tsakanin mutaken da ke aikin hakar zinare.

“Kuma ga shi likitocin da ke ba mu tallafi a asibitocin mu an kwashe su.”

A daya daga cikin asibitocin da MSF ke gudanar da aikaceaikacenta a garin Anka, wakilin Aminiya ya tarar da likitocin ’yan Nijeriya ne kadai ke gudanar da aikace-aikace a karkashin wannan kungiya.

Abin da ya sa MSF ta tsayar da aikace-aikaceta na wucingadi a sassan jihar Zamfara

Bincike ya nuna cewa dakatar da aikace-aikacen MSF na wucin-gadi na da nasaba ne da hare-haren ’yan bindiga da ya addabi yankunan da abin ya shafa a kananan hukumomin Anka da Zurmi.

Wani Jami’in lafiya da ke aiki a asibitin da MSF ke ba da tallafin da ke Anka wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce a lokacin da hare-haren ’yan bindiga ya yi kamari a yankin ne suka kwashe manyan ma’akatansu.

Shi ma manaja mai kula da harkar sadawarwa na kungiyar, Georg Gassauer a wata sanarwa da ya ba manema labarai ya yi nuni da cewa kungiyar ta Doctor without borders ta zabi rage ayyukanta ne a garin Zurmi a sakamakon tsanantar hareharen ’yan bindiga a watan Disamban bara.

Tarihin cutar Gubar Dalma a Jihar Zamfara

Har yanzu ana cigaba da tunawa da jimamin cutar gubar dalma wadda ta fara a shekarar 2008 wanda kuma ta yi sanadiyyar rasa rayukan yara da dama a garurun Bagega da Abare da Nasarawa da Dareta da ’Yar Galma da kananan hukumomin Anka da Bukkuyyum.

Cutar gubar dalma kamar yadda al’ummomin da abin ya shafa suke kiran ta ya fara ne a Jihar Zamfara a cikin shekara ta 2008 sakamakon aikin hakar zinare da al’ummomin yankin suke yi.

Bincike ya nuna kafin aukuwar cutur gubar dalma, ana yin aikin hakar zinare wanda ya hada da nike shi da busar da shi a cikin gidaje.

Hakan ne kuma ya haifar da matsalar gurbacewar kasar yankunan da abin ya shafa wanda ya jawo barkewar cutar.

An fara gano cutar gubar dalma ce a garin Bagega a shekarar 2008, amma lamarin ya yi kamari ne a tskanin watannin Maris da Yuli na shekarar 2010 a lokacin da cutar ta kasha kimanin mutum 163 ciki har da kananan yara 111 kamar yadda rohotannin suka nuna.

Haka kuma kimanin yara 300 suka mutu a garin ’Yar-Galma da ke Karamar Hukumar Bukkuyyum.

An gano cutar ce lokacin da ake gudanar da allurar rigakafi ga kananan yara bayan da aka gano karuwar mace-macen kananan yara a yankunan da lamarin ya shafa.

A wani rahoton da MSF ta fitar a shekara ta 2010 wanda aka yi wa lakabi da “Cutar Gubar Dalma a Zamfara” an gano gubar dalma mai yawa a jikin kananan yara kuma rahoton ya bayyana cewa wannan gubar ka iya kashe yara da manya haka kuma za ta iya haifar da tabin hankali da rashin haihuwa da cutuar koda da bari ga mata masu ciki da ma sauran cututtuka.

A sakamakon haka ne gwamnati ta gayyato masana harkar kiwon lafiya don ganin an ceto rayuwar al’ummar yankin da abin ya shafa.

A kokarin hakan ne gwamnati ta haramta duk wani aikin hakar zinare a yankunan da abin ya shafa sannan kuma aka aiwatar da aikin tsaftace yankin daga gubar.

Hakazalika, kungiyar nan ta TerraGraphics International Foundation da ke kasar Rasha ta ba da shawara ga Gwamnatin Zamfara ta wancan lokacin da a yi wa yara ’yan shekara 5 da rabi da ke yankin binciken lafiya na musamman domin sanin ko suna dauke da gubar dalma a jininsu.

Haku kuma kungiyar ta ba da shawarar da a gudanar da binciken kwakwaf a kan mutanen Bagega garin da ibtila’in gubar dalma ta fi shafa.

A sakamakon haka ne gwamnati ta fitar da kudi masu yawa a watan Fabrairun shekarar 2010 kuma a watan Maris na shekarar ta gayyato jami’an kula da lafiya na MSF domin fara aikin tantance mutanen yankin.

A lokacin gudanar da aikin likitocin sun gano cewa kusan duk yara 1, 010 da aka yi wa gwaji na bukatar kulawa ta musamman.

Haka kuma likitocin sun tabbatar yara 267 daga ciki na dauke da gubar a jininsu.

Bayan kimanin shekara 12 da kungiyar MSF ta shafe tana yaki da cutar gubar dalma a yankunan da abin ya shafa, ta hannanta aikin ga Gwamnatin Jihar Zamfara a watan Fabrairun shekarar 2022 a lokacin da ta gamsu cewa a wancan lokacin babu sauran barazanar macemace kananan yara sakamakon cutar.

MSF ta kuma bayyana cewa babban dalilin da ya jawo raguwar yaduwar cutar a yankunan shi ne shigar da kungiyoyin kasashen waje cikin yaki da cutar.

Sai dai kuma, ta nuna cewa har yanzu akwai kalubale domin shi aikin hakar zinare abu ne da ke da alaka da talauci, don haka dole matasan yankunan za su ci gaba da aikin hakar zinare.

Duk da tsanantar hare-haren ’yan bindiga da kuma hatsarin da ke tattare da sana’ar hakar zinare har yanzu akwai wuraren hakar zinare da dama da ake sana’ar a Jihar zamfara.

Binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa dimbin masu hakar zinare na ci gaba da aikace-aikacensu a kauyukan Bagega da Abare da Dareta a Karamar Hukumar Anka da ma wasu sassa na Karamar Hukumar Maru.

Daya da ke cikin masu hakar zinare a garin Maru, Ahmed Aliyu wanda ya shafe shekara 25 yana sana’ar ya ce duk da ya san akwai hatsari a tattare da sana’a, ba shi da wani zabi illa ya ci gaba.

“Dole ne mu ciyar da iyalanmu. Kuma duk wani yunkuri da za a yi domin hana mu wanna sana’a zai iya kawo barazana ga rayuwarmu domin kuwa talauci ne zai dabaibaye mu.”

Iliya Isma’ila Anka ya bayyana wa Aminiya cewa, “Duk da karuwar hare-haren ’yan bindiga har yanzu muna sana’ar hakar zinare duk da cewa ba kamar lokacin da muke da ingantaccen zaman lafiya ba.”

Shi ma Salisu Muhammad wani mai sana’ar hakar zinare da ya shafe shekara 25 a cikinta ya bayyana wa Aminiya suna kai zinarensu zuwa garuruwan Okene da Kogi da Legas da Ibadan domin sayarwa ga manyan diloli.

Ya ce “Na taba samu zinare da na sayar Naira 300,000 da Naira 400,000 da Naira 500,000 kawai ya danganta da nauyin zinaren da mutum ya samu.”

Gwamnatin Zamfara ta hana sarakuna ba da izinin hakar zinare

A watan jiya ne Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Dauda Lawal ya rattaba hannu a dokar kar ta kwana domin hana masu sarautar garjiya ciga ba da izni hakar zinare a jihar.

Sanarwar dokar ta kara da cewa an yi haka domin tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da hare-haren ’yan bindiga.