Kusan kwanaki uku ke nan da ceto ɗaliban yaran da ’yan bindiga suka kwashe daga makarantar firamare da karamar sakandaren da ke Kuriga a jihar Kaduna, har yanzu ba su haɗu da iyayensu ba.
An sace yaran ne a ranar 7 Maris, 2024 sannan aka yi nasarar ceto su a ranar Lahadi 24 ga Maris, kwanaki 16 ke nan a tsakani.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ce dai aka kai yaran da suka fito daga Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna suka gana da Gwamnan Jihar Malam Uba Sani.
- HOTUNA: Yadda daliban Kuriga suka isa gidan gwamnatin Kaduna
- Abin Da Ya Sa Ba A Cika Satar Ɗalibai Ba A Borno — Zulum
Kawo yanzu dai yara shida suna hannun sojoji suna ci gaba da karɓar magani, yayin da tun a yammacin Litinin aka damka 131 a hannun Gwamnan jihar Kaduna.
Iyayen yaran da abin ya shafa na cike da burin ganin ‘ya’yan nasu sun dawo garesu.
Adamu Abdulrauf Kuriga, mahaifin ɗaya daga cikin yaran da aka sace ya ce yana cike da mararin ganin ɗiyarsa, ganin cewa ya kwashe sama da sati biyu bai haɗa ido da ita ba.
“Har yanzu muna jiran karɓar yaranmu, saboda ba mu gansu ba tun lokacin da aka sace su. Duk da mun san suna wurin gwamnati, za mu so a dawo da su gida. Wannan shi ne farin cikinmu.”
Adamu ya jinjina wa gwamnati da kuma jami’an tsaro bisa wannan namijin ƙoƙari da ya ce sun yi wurin dawo da yaran cikin aminci.
Ita ma a nata bangaren wata mai suna Hadiza mahaifiyar Safiya, ɗaya daga cikin yaran ta bayyana farin cikinta da ceto ɗaliban, tana mai fatan gwamnati ta gaggauta damka musu ’ya’yansu.
Dagacin Kuriga, Jibril Gwadabe Kuriga ya bayyana mana cewa akwai ɗiyarsa a cikin waɗanda aka sace, cikin yardar Allah kuma aka dawo da ita.
Ya ce, ya je gidan gwamnatin Jihar Kaduna ranar Lahadi 24 ga Maris domin karɓar yaran, sai dai ba a kawo su ranar ba ba.
“Abin da ya kai ni gidan gwamnatin Jihar Kaduna ranar Lahadi shi ne in karbo yaran, to amma ba a kawo su ba a lokacin. Ina fata a damka mana ’ya’yanmu, wannan shi ne fatana.”
Binciken mu ya gano cewa ɗaliban da aka ceto suna karkashin kulawar ma’aikatar jin daɗi da walwalar jama’a ta Jihar Kaduna, kuma suna samun cikakkiyar kulawa a wata cibiya da ke jihar daga jami’an tsaron ke kula da su.