Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ), ta bayyana yadda dakarunta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro suka ceto ɗalibai 137 da aka sace a Makarantar Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Daraktan Yada Labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce ɗaliban da aka ceto sun haɗa da mata 76 da maza 61 a safiyar wannan Lahadi, 24 ga watan Maris 2024, a wani wuri a Jihar Zamfara.
- Dalilin da na mayar da N10m da aka yi kuskuren turawa asusuna — Mai POS
- Zaɓen Shugaban Ƙasa ya ɗauki harama a Senegal
Ceto ɗaliban na Kaduna dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 da sojojin suka ceto ɗaliban tsangaya 16 tare da wata mata da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Gada ta Jihar Sakkwato.
Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga sun sace ɗaliban makarantar Kuriga kimanin 287 da kuma wani malaminsu da suka kada daji kwanaki aƙalla 16 da suka gabata a Jihar Kaduna.
Bayan garkuwa da su ne ’yan bindigar suka buƙaci Naira biliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa tare da sanya wa’adin ranar 27 ga watan Maris da muke ciki ko kuwa su fara kashe su ɗaya bayan ɗaya.
Da yake karin haske a safiyar wannan Lahadin, Daraktan Yada Labaran, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce adadin ɗalibai 137 kaɗai suka ceto da suka ƙunshi maza 76 da kuma mata 61.
Sai dai babban jami’in sojin bai yi wani ƙarin haske kan ko an biya kuɗin fansa ko kuma akasin haka ba.
Sai dai ya bayyana cewa dakarun sojin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na cikin gida da hukumomin gwamnati ne suka yi aiki kafada-da-kafada wajen ceto ɗaliban a wani dajin Zamfara.
Da wannan sanarwar Aminiya ta fahimci cewa, har yanzu akwai ragowar ɗalibai 150 da suka maƙale a hannun ’yan ta’addar.
Manjo Janar Buba ya ce a yayin da rundunar sojin ta miƙa wa Gwamnatin Jihar Sakkwato ɗaliban da ta ceto, daga bisani za ta miƙa wa Gwamnatin Jihar Kaduna.
Ya ƙara da cewa, nasarorin da sojojin ke samu a baya-bayan nan wata shaida ce ta ƙudirin da suka ɗauka na kuɓutar da duk waɗanda aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar nan, tare da bayyana cewa irin wannan ƙoƙari suke yi domin zakulo ɓata-garin da suka kashe sojoji a Jihar Delta.
Aminiya ta ruwaito cewa, a farkon wannan wata na Maris ne wasu ’yan bindiga suka yi wa makarantar firamare da ƙaramar sakandiren Kuriga — da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna — ƙawanya tare da awon-gaba da wasu ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, kodayake shi malamin ya samu kuɓuta.
A lokacin da gwamnan Jihar Uba Sani ya kai ziyara garin, malamin da ya kuɓuta Abubakar Isah ya shaida masa cewa, maharan sun zo makarantar ne daidai lokacin da aka kammala taron ɗalibai wato Assembly.
Malamin ya ce an ɗauki ɗaliban makarantar sakandire kimanin 187, sai kuma na Firamare 125, aka kaɗa su daji, sai dai malamin ya ce da suka fara tafiya shi da wasu ɗalibai kimanin 25 sun kuɓuta.
Tun bayan sace ɗaliban ne dai Shugaba Tinubu ya bai wa hukumomin tsaron ƙasar umarnin ganin an kuɓutar da ɗaliban, sai dai ya ce duk rintsi babu ko sisin kobo da za a biya a matsayin kuɗin fansa.