Dakarun sojin Nijeriya sun yi nasarar kashe wasu ’yan ta’adda yayin wani samame da suka kai garin Kunchin Kalgo a ƙaramar hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara.
A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, ta ce a ranar 10 ga watan Yuni ne rundunar FANSAN YAMMA ta kashe ƙasurguman ‘yan ta’addan da suka haɗa da Auta da Abdul Jamilu da kuma Salisu.
- Leroy Sane ya koma Galatasaray
- Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu
“Waɗannan ’yan ta’adda suna da alaƙa da ayyukan tashin hankali da ta’addanci da ake yawan samu a yankin gaba ɗaya.
“Wannan farmakin dai na nuni da wani gagarumin koma baya ga masu aikata laifuka, wanda ke dagula zaman lafiya da tsaro a yankin,” in ji sanarwar.
Bayanan sirri na farko-farko sun nuna cewa an kashe ƙarin wasu shugabannin ’yan ta’adda, ciki har da wani da aka fi sani da Babaye a lokacin harin.
Kazalika, a wani lamarin daban, rahotanni sun ce an kashe Sale Ado Madele da aka fi sani da Sarki, babban ɗan shugaban ‘yan bindiga Ado Alieru.
A wani lamarin mai kama da haka, sojojin sun kuma kashe wasu ’yan ta’adda goma da suka taru a kusa da wata tashar mai da ke garin Danjibga.
Ana kyautata zaton ‘yan ta’addan na cikin wani gungun hadin-gwiwa da Dogo Sule ya haɗa domin kai hari.
Rundunar sojojin Nijeriya ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da kuma maido da dauwamammen zaman lafiya a fadin Jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.
“Wannan aiki yana ƙara jaddada ƙudurinmu na wargaza hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda tare da gurfanar da masu aikata laifuka a gaban ƙuliya.