Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gurfana a gaban wata kotun tarayya da ke birnin Miami na Jihar Florida don ya fuskanci zarge-zargen da ake masa.
Ana dai zargin tsohon shugaban ne da wasu jerin tuhumce-tuhumce har guda 37 masu alaka da boye wasu muhimman takardu, zamanin da yake mulki.
- A kokarin tserewa, mai garkuwa da mutane ya yanke jiki ya fadi ya mutu
- Gwamnan Ondo ya mika wa Mataimakinsa mulkin Jihar, ya tafi neman lafiya
Sai dai yayin zaman kotun na ranar Talata, cincirindon magoya bayansa ne suka taru a wajen kotun don nuna goyon bayansu gare shi.
Amma an jibge tarin jami’an tsaro a kewayen kotun, inda aka hana magoya bayan nasa da ma sauran jama’a shiga ciki saboda tsaro.
Trump, wanda ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa neman shugabancin kasar a zaben shekara ta 2024 mai zuwa, ya sha bayyana shari’ar da ake yi masa da bi-ta-da-kulli.
Ana dai sa ran zai yi jawabi ga magoya bayansa da yammacin Talata a Bedminster da ke birnin New Jersey, bayan kammala zaman kotun.