✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar

China ta mayar da martani da ƙarin haraji har kashi 125% kan kayayyakin Amurka.

Gwamnatin Amurka ta sanar da janye sabon harajin da ta ƙaƙaba wa kayayyakin laturoni irin su wayoyin salula, kwamfutoci da sauran na’urorin da ake shigo mata daga ƙetare.

Ana sa ran matakin ya rage raɗaɗin tashin farashin kayayyakin da zai faru a Amurka bayan da a kwanaki Shugaba Donald Trump ya lafta wa ƙasashe ciki har da China haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar.

Sai dai gwamnatin ta Amurka wacce ta sanar da sassaucin ta hannun hukumar kwastam ba ta bayyana dalilin cire harajin ba.

Amma dai ana sa ran kamfanonin fasaha na Amurka kamar Apple da Dell za su ci gajiyar hakan matuƙa, ganin yawancin kayayyakinsu ana haɗa su ne a China.

Trump ya janye harajin wayoyi da kwamfutoci.

Bayanai sun ce sassaucin na zuwa ne bayan kamfanonin fasahar zamani na Amurkan sun koka kan yadda na’urori za su yi tashin gwauron zabi, saboda yawancinsu daga China suke sayensu, musamman ma iPhone da kusan kashi 80 na wayoyin Amurkawa ke amfani da su.

Masana sun ce wannan sauƙin zai rage hauhawar farashi da kuma matsin da masana’antar harkokin fasahar zamani ke fuskanta.

Tuni China ta mayar da martani da ƙarin haraji har kashi 125% kan kayayyakin Amurka da ke shiga ƙasar.