✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu

Kotun ta ce babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da bayyana wa jama’a ba.

Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin a ranar Talata, yana mai cewa babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da an bayyana wa jama’a ba.

A watan Yunin 2023 ce wani Ba’Amurke, Aaron Greenspan, a ƙarƙashin dokar ’yancin fitar da bayanai (FOAI) ya miƙa buƙatar a ofishin zartarwa na lauyoyin Amurka, da Hukumar FBI da Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (DEA) da kuma Hukumar Leƙen Asiri ta (CIA).

Wasu bayanai na cewa, a shekarar 1993 ce Tinubu ya sarayar da kimanin Dala 460,000 ga gwamnatin Amurka bayan mahukunta sun alaƙanta kuɗin da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ana iya tun cewa, wannan hujja ta rashin cancantar tsayawa takara manyan ’yan adawar Shugaba Tinubu — Atiku Abubakar da Peter Obi — suka gabatar a yayin ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Sai dai kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen ta yi watsi da ita tana mai tabbatar da nasarar Tinubu a babban zaɓen ƙasar ma 2023.