Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da duka shirye-shiryen yaƙi da talauci na hukumar NSIPA nan take.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya fitar, ta ce an ɗauki matakin ne domin gudanar da bincike kan zargin badaƙala tsakanin jagorancin hukumar da kuma yadda take gudanar da shirye-shiryenta.
- Ina farin ciki da godiya da addu’o’in Kanawa — Abba Gida-Gida
- Abubuwan da suka faru a Kotun Koli a Shari’ar Gwamnan Kano
Sanarwar ta ce an dakatar da duka shirye-shirye huɗu da hukumar ke jagoranta, kama daga shirin N-Power, da biyan kuɗaɗen tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi da tallafa wa masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i da shirin ciyar da ɗaliban makarantun firamare.
Sanarwar ta ƙara da cewa a matakin farko dakatarwar ta mako shida ce, kafin a kammala bincike kan batun.
Shugaba Tinubu ya kuma nuna damuwa kan samun kura-kurai a yadda ake tafiyar da shirye-shiryen musamman biyan kuɗi ga mutane da ke amfana da shirye-shiryen hukumar.
Shugaban ƙasar ya kuma kafa kwamitin dai zai gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar da nufin samar da sauyin da ake buƙata a ayyukan hukumar.
“Don haka an dakatar da duka ayyukan hukumar da suka haɗar da gudanarwa da biyan kuɗaɗe da yin rajista,” in ji sanarwar
Sanarwar ta ci gaba da cewa shugaba Tinubu na son tabbatar wa ’yan ƙasar da masu ruwa da tsaki, cewa a shirye gwamnatinsa take wajen tabbatar da gaskiya da adalci kan shirye-shiryen hukumar musamman kan niyar da aka kafata, na amfanar da masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.
A Talatar makon jiya ce Shugaba Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Ba da Tallafin Dogaro da kai ta ƙasa (NSIPA), Halima Shehu kan zargin almundahana.
Tinubu ya dakatar da ita ne bayan zargin aikata zamba a hukumar sannan ya ba da umarnin za a gudanar cikakken bincike kan zargin da ake mata.
Kazalika, ya kuma da ba da umarnin maye gurbinta da Mista Akindele Egbuwalo a matsayin mukaddashin shugaban hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken.