✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da suka faru a Kotun Koli a Shari’ar Gwamnan Kano

Kotun Koli ta shawarci alkalai su rika yin duba na tsanaki kan kararrakin da aka kawo gabansu kafin su yanke hukunci

A yau Juma’a 12 ga Janairu 2023 Kotun Koli ta tabbatar da Gwamnan Kano Abba Kabir Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a kan kujerarsa.

Kotun ta soke hukunce-hukuncen da kotunan baya suka yanke na kwace kujerar Abba da kuma ba wa babban abokin hamayyansa, Nasir Yusuf Gawuna jam’iyyar APC.

Kotun Koli ta sanar da hukuncin ne bayan yi watsi da kararrakin da APC ta shigar na zargin aringizon kuri’un bogi dubu 165 da kuma ikirarin cewa Abba ba halastaccen dan NNPP ba ne, da ke da hurumin shiga zaben na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Alkalin da ya karanta hukuncin, Mai Shari’a Inayng Okoro, ya sanar cewa kotun daukaka kara ta yi kuskure wajen soke kuri’un Abba da ake takaddama a kan sahihancinsu, hasali ma, babu hujjar da ta tabbatar cewa ba su ne aka jefa a zaben ba.

Hakazalika, alkalan na kotun kolin sun sanar cewa batun zaman Abba dan takarar gwamna a NNPP abu ne na cikin gidan jam’iyyar, don haka wanda ba dan jam’iyyar ba shi da hurumin kalubantar zamansa dan takarar jam’iyyar.

Da yake soke hukunce hukuncen na farko, Mai Shari’a Okoro ya shawarci alkalai da su rika yin duba na tsanaki kan kararrakin da aka kawo gabansu kafin su yanke hukunci.

Hukuncin kotun karshen na zuwa ne kawanaki 298 da zaben Gwamnan Kano, wanda aka shafe sama da makonni 40 ana shari’a a kansa.

Shari’ar dai ta samu asali ne da karar da APC ta shigar gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano tana kalubalantar nasarar Gwamnan Abba, inda take neman a ayyana Gawuna a ma Abba.

Gwamna Abba da NNPP ne suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a wannan shar’a mai cike da rudani ne domin ƙalubalantar ƙwace kujerarsa da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ta yi.

Suna kuma kalubalantar yi da kuma shirinta na sauya rubutaccen hukuncinta — mai karo da juna — da ya tabbatar masa da kujerar.

Karo na biyu ke nan da gwamnan Kanon ke daukaka kara kan shari’ar, da nufin kare kujerarsa, da kuma rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano  da  kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya  da suka kwace kujerarsa.

Shari’ar zaɓen dai ta shafe sama da kwanaki 300 tana ɗaukar hankalin jama’a, musamman ma bayan kundin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya kan shari’ar ya fito ɗauke da saɓanin hukuncin da aka karanta a zamanta.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta gwara kan jama’a

A hukuncin da kotun ta karanta, ta sanar da ƙwace kujerar gwamnan a bisa hujjar cewa shi ba ɗan Jam’iyyar NNPP da ya lashe zaɓe a ƙarƙashin inuwarta ba ne, saboda babu sunansa a rajistar mambobin NNPP da jam’iyyar ta miƙa wa Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC).

Wannan wata sabuwar sarƙaƙiya ce, kasancewar a hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta yanke a watan Satumba, ta bayyana cewa ba ta da hurumi a kan wannan zargin da Jam’iyyar APC ta yi, domin lamari ne na gabanin zaɓe.

Amma Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce kotun farkon ba ta yi aikinta ba, domin kuwa tana da hurumi kan batun halascin takarar Abba a NNPP.

A saboda haka, kotun ɗaukaka ƙarar ta kwace kujerar domin, a cewarta, kujerar ba ta halasta a gare shi ba, domin kuwa INEC ba ta san shi a matsayin ɗan NNPP ba a lokacin zaɓen, don haka ba yadda za a yi ya zama ɗan takarar jami’yyar da shi ba ɗanta ba ne, ballantana ya ci mata zabe.