✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taurarin Zamani: Adnan Mukhtar Tudun Wada

Adnan matashin ɗan siyasa ne da sunansa ya yi shura a tsakanin sa'aninsa.

Adnan matashin dan siyasa ne kuma dan gwagwarmaya, wanda ya yi ƙaurin suna a Soshiyal Midiya.

Ya ce ba zai taba mantawa ba da yadda waɗanda ya ɗauka masoyansa ne suka riƙa murna kan faɗuwarsa a zaben fidda gwani gabanin Zaɓen 2023.

Kazalika, Adnan ya ce ya gano cewar burinsa ba zai cika ba idan ya tsaya a tafiyar Kwankwasiyya, saboda ita daman siyasa kasuwar buƙata ce.

A gefe guda kuma, ya ce ya ɗauki darasi a tafiyar siyasa da ya yi, kuma zai gyara wuraren da ya samu kuskure domin cikar burinsa a gaba.

Kalli hirar da shirin Taurarin Zamani ya yi da shi don ganin yadda ta kaya.