Gwamnatin Taliban a Afghanistan na bikin cika shekara biyu da sake karbe ikon kasar.
Tun da sanyin safiyar Talata ayarin motocin dakarun Taliban suka fara taruwa domin yin fareti a Dandalin Massoud da ke kusa da tsohon ginin Ofishin Jakadancin Amurka a birnin Kabul.
Albarkacin bikin, an kawata birnin Kabul da sabuwar tutar Daular Musulunci ta Afghanistan — sabon sunan da kungiyar ta sanya wa kasar — a yayin da aka girke jami’an tsaro a muhimman wurare a sassan kasar.
Wasu daga cikinsu sun yi ta daukar hotunan selfie, magoya bayyan kungiyar na ta wasa da babura dauke da tutar kasar, masu sayar sayar da sabuwar tutar kasar da kungiyar ta sauya bayan dawowarta kuma suke cin kasuwarsu.
A yankin Herat da ke Yammacin kasar, magoya bayan Taliban sun rika wake-waken kin jinin “Amurka da kasashen Turai tare da jaddada mubaya’arsu ga Dular Musulunci ta Afghanistan.”
Shugabannin sun kuma lashi takobin yakar duk wata barazana ga ’yancin kasarsu da suka sake karbewa shekara 20 bayan dakarun Amurka da sauran kasashen sun murkushe gwamnatinsu a shekarar 2001.
A ranar 15 ga watan Agustan 2021 ne Taliban ta sake cin birnin Kabul da yaki bayan janyewar dakarun Amurka.
Kazamin harin da kungiyar ta kai ta kwace ikon birnin ya sa tsohon shugaban kasar da mukarrabansa da ma dubban daruruwan ’yan kasar tserewa neman mafaka a wasu kasashe.
– Afghanistan bayan dawowar Taliban –
Shekara biyu na dawowar Taliban a Afghanistan sun kasance masu cike da ce-ce-ku-ce, saboda gwamnatin ta dawo da wasu tsauraran dokokin Musulunci da kasashen duniya ke ganin tauye hakkin mata ne.
Amma a gwamnatin ta fitar na zagayowar kwace kasar, ta yaba da nasarar da ta samu da ya “ba da damar kafa tsarin addinin Islama a Afghanistan.
“Sake karbe ikon Kabul tabbaci ne cewa babu mai iya danne kasarmu ya zauna a cikinta,” inji sanarwar da gwamnatin ta fitar da cewa “babu wani mai kutse da za mu bari ya yi wa Afghanistan mulkin mallaka.”
– ‘An soke bikin a Khandahar’ –
Duk da cewa an gudanar da bikin inda sojoji suka yi fareti a sassan kasar, an soke bikin a birnin Kandahar, cibiyar Taliban kuma fadar shugabanta, Hibatullah Akhundzada.
Akhundzada da kansa ne ya sanar da soke faretin domin kada a takura wa ala’umma, kasancwar da farko an shiya gudanarwa har da motocin da dakarun Amurka suka bari.
A birnin Kabul kuma, ma’aikatar ilimi ta shirya bikin a wata makaranta, wanda kuma ya samu halarcin jakadun kwasu kasashe — duk da cewa har yanzu kasashen duniya ba sa daukar Taliban a matsayin halastacciyar gwamnati.
– ‘Ya kamata mu yi murna’ –
Wani dalibi da ke karatun likitanci a Jami’ar Kabul, Mortaza Khairi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa zagayowar ranar abin su yi murna ne.
“Yau shekara biyu ke nan da kawo karshen mamayar da aka yi wa kasarmu, don haka wannan babban abin mu yi murna ne,” in ji shi.
Kawo yanzu dai kasashen duniya na yin kaffa-kaffa kan yin hulda da Taliban saboda zargin dokokinta sun tauye hakkin mata —na fitowa bainar jama’a da zuwa makaranta — lamarinda ya hana kasashen ba ta tallafi.
A ranar Litinin wasu kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun caccaki Taliban kan saba alkawarin da ta yi na sassauta tsauraran dokokinta na lokaci mulkinta na farko (1996 zuwa 2001) a Afghanistan.
– ‘Zanga-zangar matan Afghanistan –
Al’ummar kasar kuma na nuna damuwa game da matsin tattalin arziki da kasar ke fama da ita tun bayan da Taliban ta karbe iko, kasashen duniya suka sanya mata takunkumin karya tattalin arziki.
Wani manomi, Rahatullah Azizi ya ce a baya yana iya noma amfani mai yawa da yake iya dogaro da kansa, amma yanzu sai dai abin da shi da iyalansa za su ci.
– Sha’anin tsaro –
Amma ya ce duk da haka, an samu ingantuwar tsaro a kasar, domin zai iya zuwa duk inda ya ga dama a cikin dare ba tare da wata fargaba ba.
Duk da cewa an samu tsaro a Afghanistan a shekara biyu na Taliban, kungiyar IS na ci gaba da zama babbar barazana ga makwabciyarsu, Pakistan.
Taliban ta yi alkawarin kasar Afghanistan ba za ta zama mafaka ga masu tayar da kayar baya ba don kai hari a wasu kasashe, sai dai har yanzu hakan bai samu ba.
A yayin da wasu al’ummar Afghanistan ke bikin karewar yaki da kuma dawowar Taliban, wasu na ganin zagayowar ranar 15 ga watan Agusta a matsayin ranar bakin ciki.