✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta sa wa matan jami’a dokar sanya nikabi

Taliban ta kafa dokar raba ajujuwan maza da na mata.

Kungiyar Taliban ta kafa dokar da ta wajabta wa mata a jami’o’i masu zaman kansu a kasar Afghanistan sanya nikabi tare da rabe ajujuwan maza da na mata.

Dokar da hukumomin ilimin Taliban suka fitar ta cikin wata sanarwa ta ce malamai mata ne kadai aka yarda su koyar da dalibai mata, idan kuma babu malamai mata, sai tsofaffi maza da aka aminta da halayensu su koyar da su.

Wannan dokar na zuwa ne daidai lokacin da ake shirin bude makarantu domin fara karatu a ranar Litinin.

Dokar ta kuma shafi jami’oi da manyan kwaleji masu zaman kansu wadanda suka sauya alkiblarsu bayan kifar da gwamnatin Taliban a 2001.

A lokacin mulkin Taliban na baya, an ’yan mata ba sa zuwa makarantu saboda dokar hana su zama aji tare da maza da kuma wajibcin samar musu da dan rakiya daga cikin ’yan uwansu kafin su bar gida.

Sabuwar dokar dai ba ta wajabta wa matan sanya nikabi mai rufe daukacin fuskokin mata ba kamar yadda a baya ake yi.

Bayan hambarar da Taliban a shekarun baya, an daina amfani da nikabin da ke rufe daukacin fuskar mata a birnin Kabul bayan, in bada wasu garuruwa da kauyukan kasar.