✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta mutu tana saduwa da saurayinta da ya sha maganin karfin maza

Saurayin dai ya sha maganin ne don ya birge ta

Wata mata ta mutu tana tsaka da saduwa da saurayinta da ya sha maganin karfin maza domin ya birge ta a Jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne tsakanin saurayin mai suna Isaac da budurwar tasa a wani otal da ke yankin Temidire a Ilorin, babban birnin Jihar.

Bayanai sun nuna Isaac, wanda yake da shagon yin aski dai ya sha maganin ne da nufin birge budurwar tasa.

Wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Lokacin da suke saduwar, matar ta yi korafin cewa ta gaji, sannan jini na fitowa daga gabanta.

“Ana cikin haka ne aka ga ta daina motsi, inda aka garzaya da ita asibiti, kuma ta mutu a can.”

Wakilinmu ya kuma gano cewa bayan faruwar lamarin, saurayin ya jawo hankalin ma’aikatan otal din domin su kai masa ɗauki.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Ajayi Okasanmi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce, “muj kama saurayin sannan mun fata bincike domin gano ainihin abin da ya faru tsakanin shi da ita.”