Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya ba wa dakarun rundunar wa’adin wata guda su fatattaki sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta Mahmud a da ta ɓulla a Jihar Kwara.
Oluyede ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a ziyarar da ya kai Barikin Sobi da ke Ilorin, babban birnin jihar.
“Daga wata mai zuwa, ba na son in ƙara jin mostin waɗannan ’yan ta’addan a yankin Dam ɗin Kainji,” in ji babban hafsan sojin.
Ya umarce su da su kawar da ’yan ta’addan daga ƙananan hukumomi biyun da suka addaba, yana mai jaddada cewa yana son a kammala aikin cikin wata mai zuwa.
- Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan rediyo na haɗin gwiwa
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci
Babban hafsan sojin ya ce Najeriya ba za ta iya ba da damar ’yan fashin daji ko ’yan ta’adda su ƙara yaɗuwa zuwa wani ɓangare na ƙasar ba.
“Don haka, kuna nan kuma na san za ku yi hakan don tabbatar da cewa waɗancan mutanen sun bar mana wannan wurin,” kamar yadda ya shaida wa sojojin.
“Idan suna son shiga wata ƙasa, wannan su ta shafa, amma dole ne ku kawar da su daga waɗannan dazuzzukan don kada mu sake samun wata ƙungiyar Boko Haram da za ta dame mu a nan.
“Ina iya gaya muku, cikin wata mai zuwa, al’amura za su bambanta. Abin da ke faruwa a Kwara ba zai iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya gaba ɗaya ba; lamari ne keɓantacce kuma za mu magance shi kai tsaye.”