✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na buƙaci a daina biya na kuɗin fansho da alawus-alawus na tsohon gwamna — Ɗankwambo

Wannan lamari ba kansa farau ba a cewar Daraktan Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Gombe, Ismai’la Misilli.

Sanatan Gombe ta Arewa, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, ya buƙaci a dakatar da biyansa kudaden fansho da alawus-alawus da ya kamata a biya shi a matsayinsa na tsohon gwamna.

Sanata Dankwambo, wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Gombe, ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da sa hannunsa da ya aike wa Gwamnatin Jihar.

A takardar mai ɗauke da kwanan watan 28 ga Satumba, Dankwambo ya ce ya buƙaci hakan ne duk da cewa Dokar Fansho ta 2007 da aka yi wa gyaran fuska ta tanadi hakan.

A cewarsa, wannan mataki na zuwa ne bayan ya shawarar da kungiyoyin fararen hula, hukumomi da abokansa suka ba shi kan dakatar da karɓar kuɗin.

Dankwambo, ya ce ya rubuta takardar ce yana mai neman gwamnati ta tsayar da biyansa fansho da alawus-alawus da yawan kudin ya kai naira 694,557.82 duk wata.

Ya kuma ce ya dace a biya shi a matsayinsa na tsohon gwamna, amma tunda ya bar ofis a shekarar 2019, bai taba amfanuwa da wani alawus ba kama daga na jinya, na kayayyakin gida (furniture) ko na abun hawa da sauran su.

Wakilinmu ya tuntubi Babban Daraktan Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, inda ya ce ba su samu takadar ba domin babu hatimin gwamnati na shaidar an karbi takardar.

Sai dai ya ce watakila mutanen tsohon gwamnan ne suka tura takardar a yanar gizo kawai ba tare da sun isar da ita wa gwamnati ba.

Isma’ila Misilli, ya kara da cewa “ai ba akan Dankwambo kadai aka fara daina biyan tsofaffin gwamnoni fansho da alawus-alawus ba.

“Duk wanda ya yi Gwamna kuma daga baya ya zama Minista ko Sanata, suna daina karɓar kuɗin domin bai dace ana biyanka albashin Sanata ko Minista kuma kana karɓar fansho ba,” a cewarsa.

Sai dai Misilli ya ce yana ganin irin shawarwarin da ake ba su ne ya sa suke daina karba, shi ma Ɗankwambo yabi sahu wanda kuma yin hakan shi ne daidai.