Wata tsohuwa ’yar kasar China mai suna Liu ta yanke shawarar barin dukiyarta da ta kai kudin China Yuan miliyan 20, kimanin Dalar Amurka miliyan 2.8 wanda ya yi daidai da Naira biliyan 2 da dubu miliyan 548 ga kare da kyanwarta, inda ta ce a koyaushe suna wurinta, sabanin ’ya’yanta uku.
Matar, ta yi wasiyyar ta farko ne a shekarun baya, inda ta raba abin da ta mallaka a tsakanin ’ya’yanta uku, amma a kwanan baya ta canja tunani bayan da ta ce ’ya’yanta sun yi watsi da ita.
- Almundahanar N21.5bn: Kotu ta kori karar da aka shigar da tsohon hafsan sojin sama
- Rikicin Filato: Ƙungiyar Izala ta raba kayan agaji a Mangu
Ta yi ikirarin cewa ’ya’yanta ba su taba ziyartarta ba, ko kuma ba su shirya yadda za a kula da ita a lokacin da take rashin lafiya.
Kuma ba su taba haduwa da ita ba, don haka ta yanke shawarar barin duk abin da ta mallaka ga dabbobin biyu da suke gefenta a koyaushe. Ta ce kyanwa da karen su ne suka damu da ita.
Matar wadda ke zaune a birnin Shanghai a kasar China tuni ta sauya wasiyyarta ta yadda za a yi amfani da duk kudinta wajen kula da dabbobinta da zuriyarsu bayan rasuwarta.
Abin takaici ga matar Liu, dokar kasar China ta hana mutane barin kayansu kai-tsaye ga dabbobinsu.
Duk da haka, bayan tuntubar lauya, Liu ta samu hanyar da za ta bi – ta zabi hukumar asibitin dabbobi a matsayin mai kula da dukiyarta, tare da ba da amanar kula da dabbobin da take kauna.
Jami’in hedikwatar cibiyar rajista ta kasar China da ke birnin Beijing, mai suna Chen Kai, ya shaida wa jaridar South China Morning Post cewa, halin yanzu na Liu za ta jefa kadarorinta cikin hadari.
Ya ce ofishinsa ya umarce ta kan ta nada wanda ta amince da shi da zai kula da asibitin dabbobin ta yadda zai rika kula da dukiyar gadon.
“Wasiyyar Liu a halin yanzu hanya daya ce, kuma mun ba ta shawarar ta nada wanda ta amince da shi don kula da asibitin dabbobi don tabbatar da kula da dabbobin yadda ya kamata,” in ji Chen Kai.
Wani kwararre kan harkokin shari’a ya bayyana fatansa cewa ’ya’yan Liu za su zo koma gare ta, kuma za ta canza ra’ayi game da mayar da dabbobinta su zama magadanta.
Labarin tsohuwar ya ratsa zukatan miliyoyin mutane a kasar China, wadanda akasarinsu sun ji tausayin halin da take ciki. Irin hakan babban lamari ne a Asiya kuma ’ya’yan da suka yi watsi da iyayensu a lokacin da suka tsufa suna fuskantar shari’a.