✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Noman rake: Najeriya da China sun kulla yarjejeniyar kasuwancin $1bn

Kamfanin SINOMACH zai kafa masana'antar sukari da kuma gonar rake da za su fara da samar da metrik ton 100,000 na sukari a duk shekara

Hukumar Bunƙasa Noman Sukari a Najeriya (NSDC) ta sanya hannu kan yarjejeniyar Dala biliyan guda da kamfanin SINOMACH na ƙasar China kan bunƙasa noman rake da sarrafa shi da nufin samar da sukari da kudina ya kai metrik ton miliyan guda.

Kulla yarjejeniyar wani ɓangare ne na shirin Kawancen Najeriya da China, na Gwmanatin Shugaba Bola Tinubu, da nufin kawo masu zuba jari na kimanin Dala biliyan guda a ɓangaren sukari a Najeriya.

Daga cikin yarjejeniyar, Kamfanin SINOMACH zai kafa masana’antar sukari da kuma gonar rake da za su fara da samar da metrik ton 100,000 na sukari a duk shekara.

Kamfanin zai kuma taimaka da kwarewarsa da kayayyakin aikinsa wajen zartar da abubuwan da suka danganci gine-gine sayayyan kayan aiki da ayyukan injiniyarin. Uwa uba, zai samar da kudaden ayyukan.

A gefe guda kuma Hukumar NSDC za ta taimaka wajen samar da duk takardu da kuma sahalewar gwamnati da ake bukata domin fara aiki.

Da yake jawabi a taron sanya hannun a Abuja, Shugaban Hukumar, Kamal Bakrim ya bayyana cewa shekarar 2025 za ta kasance kashin baya ga samun bunkasar Najeriya.

“Shekara ce da muke sa ran samun gagarumar ci-gaba musamman a fannin tattalin arzikin da samar da wadataccena abinci a kasarmu.