✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida

Kimanin wata guda ke nan tana zaune a cikin ƙaramin banɗakin.

Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533.

Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi?

Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi a cikin masana’antar kayan cikin gidaje da take aiki.

Matar mai shekara 19 ta bayyana cewa, ta fito daga dangi matalauta kuma ba za ta iya biyan sama da Yuan 800 kwatankwacin Naira dubu dari 168 da 537 don biyan kuɗin ɗakin da ya dace, don haka ta tambayi maigidanta ko za ta iya zama a banɗakin.

Wallafa rubutun nata ya yi tasiri, inda yawancin mutanen da suka yi tsokaci sun ce tana yaɗa hotuna da bidiyo ne kawai don jan hankali saboda babu wanda zai iya rayuwa a cikin irin wannan yanayi.

Sai dai maigidan matar ya yi amfani da kafar sada zumunta intanet, inda ya tabbatar da cewa, lallai tana kwana a banɗaki mai kafa 6 a masana’antarsa.

“Ta dage kan da ta ta biya ƙarin kuɗi Yuan 50 — kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533 na ruwa da wutar lantarki a kowane wata gwara ta kwana bandaki, amma ba na son daukar kudinta,” in ji shugaban matar.

Matar ta ce, maigidan nata ya yi kokarin taimaka mata ta nemo gidan haya kusa da masana’antar, amma kuɗin haya ya kai kimanin Yuan 800 ($ 110) zuwa Yuan 1,000 kwatankwacin Naira dubu dari 210 da dari 6 da 72.

A halin yanzu tana karɓar albashin ƙasa da Yuan 3,000 — kwatankwacin Naira dubu dari 6 da dubu 32 da 17, kuma tana ƙoƙarin yin tanadin kuɗi mai yawa don biyan kudin hayar gida, don haka take ganin hakan bai dace.

Har ma ya ba ta damar zama a ofis a masana’antar, amma ta yanke shawarar cewa za ta fi samun sirri a banɗakin da ba a amfani da shi.

“A wajena yanzu na samu wurin zama,” budurwar ta wallwafa a intanet cewa, “ba na so in kashe kuɗi da yawa wajen yin hayar gida. Tabbas ba zan iya jure kashe Yuan 800 don hayar gida ba.”

Bayan da sakon ya yaɗu, matar ta bayyana cewa, ta daina karatu tun tana shekara 16 domin ta taimaka wa danginta da kuɗi, wanda hakan ya sa wannan aikin ya fi mata muhimmanci.

Kimanin wata guda ke nan tana zaune a cikin ƙaramin banɗakin.

Yanayin rayuwar budurwar ya samu ra’ayoyi mabambanta a shafukan sada zumunta na kasar China, inda wasu suka yaba da ƙudurinta na yin tanadin kuɗi, wasu kuma na cewa, lafiyarta ta fi kuɗi muhimmanci, kuma babu wanda ya isa ya rayu cikin wannan yanayi sai dai idan ba shi da wata mafita.