✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa

Wata koutun soja ta yanke wa wani jami’inta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa.

Wata kotun soji ta yanke wa wani kurtun soja hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa.

Kotun da ta zauna a Hedikwatar Runduna ta 82 da ke Enugu, ta yanke wa Private Adamu Mohammed hukuncin kisa kan laifin budurwar taas mai suna Hauwa Ali.

Da yake sanar da hukuncin, Shugaban kotun, Birgediya Sadisu Buhari, ya ce, “Kotun Soja ta Kasa ta yanke hukuncin cewa sojan da ake tuhuma, mai lamba 21NA/80/6365 Private Adamu Mohammed, an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa tuhumar kisan kai.”

Mukaddashin kakakin Rundunar, Jonah Unuakhalu, ya ce kwamitin kotun  ya cimma matsaya ɗaya bayan nazari mai zurfi na shaidu, tarihin aikin wanda ake tuhuma, da kuma roƙon sassauci daga lauyansa.

Ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa kotun sojan, ta kuma yanke wa wani Soja mai suna Private Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru 10 a kurkuku saboda samun sa da laifin fashi da makami a wani shahararren kantin sayayya a Enugu.

Ya kara da cewa an yanke wa waɗannan mutane biyu hukuncin ne bayan kammala shari’o’insu kan laifukan kisan kai da fashi da makami.

Babban Kwamandan Runduna ta 82, Manjo-Janar Oluyemi Olatoye, ne ya kaddamar da kotun sojin a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, domin yanke hukunci kan shari’o’in da suka shafi ma’aikatan da suka yi kuskure a cikin Rundunar.

A cewarsa, waɗannan hukunce-hukuncen sai sun samu tabbatarwa daga hukumomin soji da suka dace, wanda ya nuna ƙarshen shari’o’in sojojin.

Ya sake jaddada ƙudurin Sojojin Najeriya na tabbatar da ɗa’a da kuma kiyaye mafi girman ƙa’idoji na ɗabi’u da ƙwarewa.

“Kuskuren ayyukan wasu kaɗan ba su nuna ƙimar ƙungiyar ba. A koyaushe ana ɗaukar matakai masu sauri da kuma ƙarfi don tabbatar da riƙon amana da adalci,” in ji shi.