✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:06 na dare kuma ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa ta.

Wata gobara da ta tashi a yammacin ranar Laraba a wata shahararriyar kasuwar wayoyin salula da ke ‘Challenge Market’, a Ilorin babban birnin Jihar Kwara, ta yi mummunar ɓarna.

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:06 na dare kuma ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa ta.

Kasuwar tana da shaguna sama da 120, rumfunan 80, da wasu wuraren kasuwancin wayar da yawa. Rahotanni sun ce gobarar ta shafi rumfuna 10.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar a ranar Alhamis, ya ce gobarar ta fi shafar shagunan waya da wuraren gyara.

“Nan take jami’an kashe gobararmu suka taru suka isa wurin inda suka tarar da shaguna da dama sun ƙone da wuta,” in ji shi.

“Kasuwar ta ƙunshi shaguna sama da 120,  rumfuna 80 da sauran wuraren kasuwanci masu yawa. Ta hanyar shiga tsakani cikin gaggawa, da ƙwararrun dabaru, jami’an sun yi nasarar daƙile yaɗuwar gobarar, tare da taƙaita tasirinta zuwa rumfuna 10 kawai.

“Wuraren da gobarar ya shafa dai sun haɗa da shagunan waya da kuma wuraren gyaran waya, binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce ta tashi.

“ ’Yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a kasuwar sun yabawa hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara bisa saurin ɗaukar matakin da suka yi wajen ceto kasuwar daga gobarar da ta ɓarke.”

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Falade Olumuyiwa ya jajantawa shugabannin kasuwar da ’yan kasuwar da gobarar ta shafa.

Olumuyiwa ya kuma yi addu’ar Allah Ya dawo masu da dukkan asarar da aka samu.