✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa

Matar da ta gaisa da Mariano Grinspun, tsohuwar abokiyar karatunsa ce, amma hakan ya tunzura budurwarsa.

Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi.

Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima!

Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki.

Abin ya faru ne ranar 21 ga Oktoba 2024, kusa da titin Balboa da La Bastilla, a birnin González Catan.

Mariano da budurwarsa Natacha Palavecino, suna tafiya tare, sai suka ci karo da wata mata da ta gaida Mariano kuma ta tambaye shi halin da yake ciki.

Gaisuwar ta haukata budurwar Mariano, inda ta zaro wuƙa a ɓoye ta afka masa.

Matar da ta gaisa da Mariano Grinspun, tsohuwar abokiyar karatunsa ce, amma hakan ya tunzura budurwarsa.

Natacha ta kai hannu ta ɗauki wata boyayyiyar wuƙa sannan ta yanki matar mai suna LC kamar yadda kafafen yada labarai na kasar Argentina suka bayyana.

Bayan yankar LC da wuƙar ta faɗi kasa ta yi yunƙurin ƙara yankar ta, amma ta sa hannunta ta kare, wanda da watakila ta kashe ta da ba don wani mutumin ba wanda ya yi nasarar daƙile faruwar hakan.

Abin takaici, Mariano Grinspun bai yi sa’a sosai ba, domin bayan da ta gaza kashe matar, Natacha Palavecino ta far wa saurayin nata, inda ta daɓa masa wuƙa a kirji.

Masoyan sun yi ta muhawara ta tsawon mintuna da dama, kamar yadda kyamarorin sa ido na CCTV a yankin suka nuna, wanda a lokacin Mariano ya fadi kasa yana shure-shure.

Zuwa wani lokaci, ya kasa tashi sai budurwarsa mai shekara 32 ta kai masa hari da hannunta.

Shaidun gani da ido sun kira jami’an agajin gaggawa, amma ba su iya yin komai ba wajen ceto rayuwarsa.

Wani bincike da aka gudanar ya bayyana tarihin tashin hankali Natacha Palavecino.

A 2021, an yanke mata hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda ta dava wa wani tsohon saurayinta wuƙa a kirji, har ma Mariano da kansa ya kai ƙarar ta ga ’yan sanda saboda barazanar da ta yi masa da kuma yi masa rauni a jiki.

A watan Yulin shekarar bara ce aka ba da umarnin hana Natacha duk wata alaka da Mariano.

Sai dai bayan wucewar wa’adin, sai ya yanke shawarar sake dawowa da alakar.

Palavecino mai shekaru 32 za ta iya kasancewa a gidan yari tsawon shekaru saboda wannan laifi na kisan saurayinta da kuma yunkurin kisan matar da ta gaishe shi a kan titi.