Wasu ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wani Bakano mai suna Muktari Ibrahim, sun sako shi bayan an ba su kiret din giya shida, babur kirar Bajaj da kuma kudi N500,000.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa an yi garkuwa da mutumin ne tun ranar 21 ga watan Nuwamban 2021, tare da wasu ’yan kasuwa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
- Duniyar Ma’aurata: Matakan cim ma nasarar daren farko
- Mun kawo tsarin da za a kiwata rago da abincin N3,000 a shekara — Sarkin Muri
Sai dai an sako shi ranar Larabar da ta wuce bayan ya shafe wata uku a tsare.
Tun lokacin da suka kama shi dai, masu garkuwar sun nemi a ba su Naira miliyan 50 ne, kafin daga bisani bayan dogon ciniki su yarda su karbi kiret din giyar mai suna Lager guda shida, katan biyu na lemon Power Horse da kuma baburan Bajaj guda biyu.
Wata majiya daga iyalan mutumin ta shaida wa jaridar cewa da farko babur kirar Boxer suka nemi a ba su, amma da aka nuna musu yanzu an hana sayar da shi a kasuwa, sai suka amince za su karbi Bajaj din.
Mjiyar ta ce, “Yayin da ake cinikin sun gargade mu da kada mu kuskura mu makala na’urar bibiyar sahun mutane ko kuma mu zuba guba a cikin giyar. Hatta sayen giyar ba karamin tashin hankali ya zamar mana ba.
“Da aka kai musu kayan bayan wata azababbiyar tafiyar kasa a cikin daji, sai suka ce za su saki dan uwan namu ne kawai in suka tabbatar babu na’urar bibiyar sahu ko guba a ciki.
“Daga nan sai suka sake shi, ko kudin mota ba su ba shi ba, sai suka ce ya roka a hanya.
“A nan ne wani shugaban al’umma ya ji tausayinsa ya ba shi N300, wacce ya hau acaba da ita ya karasa Zariya,” inji wani daga cikin iyalan mutumin da ya nemi a sakaya sunansa.