✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sudan na iya fuskantar yunwa mafi muni — Amurka

Amurka ta yi kira da mayar da hankali kan halin da Sudan ke ciki.

Mahukunta a ƙasar Amurka sun yi gargaɗin cewa matsalar yunwa da ƙasar Sudan ke fuskanta na iya yin muni fiye da wadda aka taɓa fuskanta a Habasha, shekara 40 da suka gabata.

Wannan na zuwa ne, bayan da ɓangarorin da ke yi wa juna kallon hadarin kaji a ƙasar ke ci gaba da ƙazamin rikicin da suka kwashe tsawon lokaci suna fafatawa.

A cewar Jami’an na Amurka, ɓangarorin biyu, na daƙile yunƙurin shigar da kayayyakin agaji zuwa ƙasar, duk da irin ƙoƙari da ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasa da ƙasa ke yi na ganin sun shigar da kayayyaki ga sassan ƙasar.

A halin yanzu dai, hankalin ƙasashen duniya ya koma kan Gaza da ake fuskantar matsananciyar yunwa.

Sai dai mahukuntan Amurkan na gargaɗin cewa, matuƙar hankali bai koma ga Sudan ba, wadda ta shafe tsawon lokaci a jerin ƙasashen da suka fi fuskantar matsalolin jin-ƙai a duniya, na iya faɗawa tsananin yunwa.

Tuni dai yaƙin basasa na Sudan ya kashe mutane aƙalla 14,000, tare da tilastawa mutum miliyan 10 barin muhallansu.

A makon da ya gabata ne, kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya buƙaci da a kawo ƙarshen mamayar da dakarun RSF suka yi wa El Fasher, kusan wata biyu.